Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta fara makon nan da ƙarfi, inda masu zuba jari suka samu ribar kusan Naira biliyan 443 sakamakon sabon aaruwar saye da aka gani a kasuwar ranar Litinin, 13 ga Afrilu, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ci gaba ya samo asali ne daga ƙarin buƙata da aka nuna ga hannayen jari na wasu manyan kamfanoni kamar NGX Group, Trans-Nationwide Express, MC Nichols, VFD Group, CHAMS da wasu da dama.
Jimillar darajar kasuwar ta tashi daga naira tiriliyan 131.165 zuwa naira tiriliyan 131.608, wanda ke nuna ƙarin kashi 0.34 cikin ɗari, daidai da ribar naira biliyan 443.
Haka kuma, babban ma’aunin kasuwar, wato All-Share Index, ya ƙaru daga maki 203,770.43 zuwa 204,458.86, wanda ke nuna ƙarin maki 688.43, ko kuma kashi 0.34 cikin ɗari.
Wannan ci gaba ya haifar da ƙaruwa a yawan ribar da aka samu tun farkon shekarar nan (Year-to-Date), inda ya kai kashi 31.39 cikin ɗari. A ƙarshe, kasuwar ta nuna ƙarfi, inda kamfanoni 32 suka samu riba yayin da 24 suka yi asara.
A ɓangaren kamfanonin da suka fi samun riba, NGX Group ne ya jagoranci jerin da ƙarin kashi 10 cikin ɗari, inda ya rufe ciniki a kan naira 153.45. Trans-Nationwide Eɗpress ya biyo baya da kashi 9.81 cikin ɗari, yayin da MC Nichols ya samu kashi 9.74 cikin ɗari.
Haka kuma, VFD Group ya ƙaru da kashi 9.71 cikin ɗari, yayin da CHAMS ya samu ƙarin kashi 8.96 cikin ɗari a farashin hannun jarinsa.
Sai dai a ɓangaren masu asara, kamfanin Berger Paints ne ya jagoranci da asarar kashi 9.95 cikin ɗari, sai Academy da kashi 9.71 cikin ɗari, yayin da Caverton Offshore Support Group ya ragu da kashi 5.98 cikin ɗari.
Har ila yau, Honeywell Flour ya sauka da kashi 4.92 cikin ɗari, yayin da CAP ya yi asarar kashi 3.81 cikin ɗari.
Duk da wannan ci gaba, an samu raguwar yawan hada-hadar kasuwa, inda jimillar hannayen jari da aka yi ciniki da su ta ragu da kashi 14.33 cikin ɗari zuwa miliyan 470.01, tare da darajarsu ta kai naira biliyan 32.45 a cikin ma’amaloli 60,793.
Kamfanin Access Corporation ne ya fi yawan ciniki da hannayen jari miliyan 54.91, wanda ya wakilci kashi 11.68 cikin ɗari na jimillar cinikin ranar. A ɓangaren darajar kuɗi kuwa, Aradel ne ya fi, inda aka yi ciniki na naira biliyan 7.05, wanda ya kai kashi 21.74 cikin ɗari na jimillar kasuwar.
Masana tattalin arziki na ganin wannan ƙaruwa alama ce ta dawowar ƙwarin gwiwar masu zuba jari, duk da ƙalubalen tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
