17
May
Daga AISHA ASAS Rahotanni da suka bazu cikin gaggawa a kafafen sada zumunta sun jefa dubban masoya fina-finai cikin ruɗani da jimami bayan wasu bayanai sun yi iƙirarin cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Alex Ekubo, ya rasu yana da shekaru 40 a duniya. Jita-jitar ta fara ɗaukar hankali ne bayan wani saƙo da fitaccen jarumi Godwin Nnadiekwe ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana matuƙar kaɗuwa da alhini kan wani “mummunan labari” da ya ce ya samu. A cikin saƙon, ya bayyana Ekubo a matsayin baiwar da ba kasafai ake samu irinta ba a masana’antar Nollywood, yana mai…
