Daga AISHA ASAS
Labarin ciwan da ya samu ga mawaƙiya Celine Dion ya kasance tamkar gagarumar guguwa da ta taso a sararin shahara, wadda ba ta tambayar inda ya kamata ta fuskata ba. Cutar wadda ba ta yi la’akari da tarihi ko kuɗi da duk wani gata da masoya da mawaƙiyar ke da ita ba. Tabbas Annabin Rahma ya yi gaskiya, “Ka ci moriyar lafiyarka kafin ciwo”
Celine Dion ta kasance murya da ke girgiza ɗakunan kaɗe-kaɗe, ta raunana zukata, tare da samar da shauƙi na musamman. Mawaƙiyar da duniya ta yaba kuma ta amince da ta iya, har ake mata kallon wadda ba ta rasa komai da ɗan adam ke buri a duniya ba.
Kwatsam sai cuta ta musamman kamar yadda take ta musamman ta same ta. Cutar mai suna stiff-person syndrome, cuta ce da aka san da ita a ilimance, saidai kasancewarta cuta da ba kasafai ake gani ko jin wani ya kamu da ita ba, ya sa har wasu ke ƙarya wanzuwarta.
Cutar wadda masana suka tabbatar waɗanda suka taɓa kamuwa da ita ko kashi ɗaya bisa ɗari na duniya ba su kai ba, cuta ce mai matuƙar wuyar sha’ani da wahalar da wanda aka jarrabta da ita, wadda ke shafar jijiyoyin kwakwalwa da tsoka.
Haka kuma tana haddasa matsanancin ciwo da ke karya garkuwar jiki, wanda hakan ke sa a wasu lokuta mai cutar ke rasa ikon ababen da ya saba yi a baya kamar tafiya, ko tsayuwa da kansa. Kuma takan yi sanadin taɓa lafiyar murya, wadda ke sa magana ta zama mai tsada a wasu lokuta.
Wannan kuwa ya kasance babban ƙalubale ga mawaƙiyar, kasancewar ciwon ya sace mata manyan muhimman ababen da suke sa ta zama yadda take a idon duniya. Muryarta mai amo da taɓa zuciya ta fi ƙarfinta, bare kuma iya sarrafa jikinta a bainar jama’a don nishaɗantar da su.
A ‘yan kwanakin nan ne wani faifan bidiyo na mawaƙiyar ya bayyana wanda bai kasance irinsa na farko da ya taɓa fitowa ba, dalilin da ya sa wasu ke musanta sahihancinsa, saidai waɗanda suka aminta da shi sun ce ko ba ita ba ce suna da tabbacin halin da take ciki kenan, don alamomin ciwon nata kenan. Don haka a cewarsu gaskiyarsa ko akasin haka ba zai hana zuciyarsu sosuwa tare da taya masoyiyarsu da ta jima tana nishaɗantar da su jimami tare da tausaya mata ba.
A cikin faifan bidiyon wanda aka ciro daga cikin kundin rayuwarta (documentary) an hasko mawaƙiyar cikin mawuyacin hali, inda fuskarta da laɓɓanta ke rawa saboda tsananin azaba, numfashi na fita daƙyar.
Kasancewar abin gaskiya ba wasan kwaikwayo ba, ya sa zukata shiga damuwa, yayin da fuskokinsu ke hasko masu irin yadda mawaƙiyar ke rayuwa a baya. Idan ta hau dandamali don nishaɗantarwa, komai kan tsaya yayin da muryarta da gangar jikinta ke yin yadda suka ga dama, a yau kuma ita ce cuta ke ƙoƙarin ƙwace mata ikon jikinta da kuma muryarta.
Wannan kawai zai iya zama babban abin tsoro game da rayuwa, duba da irin shuhura, iko da dukiyar da mawaƙiyar ta tara, a yau duk ba su da amfani. Domin har ya zuwa yanzu, duk da tarin dukiya da alfarma da take da ita a faɗin duniya, har yau sun kasa siya mata magani guda da idan ta sha ko ta yi amfani da shi za ta samu waraka daga halin da take ciki. Asali ma a wata majiya, ana cewa, yanzu ne ma aka mayar da hankali kan cutar tare da bincike kan yadda za a iya shawo kanta da kuma magani da rigakafi tare da sanin tarihi da yadda cutar ke wanzu. Duk da cewa wasu masana sun ƙaryata hakan, a cewar su, akwai sani sosai kan cutar, kawai dai ta kasance cuta mai wuyar sha’ani. Fatan da ake yi shi ne a yi nasara tun kafin cutar ta zama sanadin barin ta duniya.
Wacce ce Celine Dion?
An haifi Celine Marie Claudette Dion a ranar 30 ga watan Maris, 1968, a ƙauyen Charlemagne na ƙasar Kanada. Ita ce ƙaramar ‘ya daga cikin ‘ya’ya 14. Inda ta taso cikin duniyar da take ciki a yanzu, wato kiɗa da waƙa. Saidai ita ce ta fi sa’a a cikinsu, domin tun tana da shekaru 12 ta fara ɗaukar hankalin duniya bayan muryarta ta isa kunnuwan Rene Angelil, wanda daga baya ya zama mijinta kuma manajanta.
Celine Dion ta zama ɗaya daga cikin mawaƙan duniya da suka fi sayar da waƙoƙi a tarihin duniya, inda waƙarta ta ‘My Heart Will Go On’ daga fim ɗin ‘Titanic’ ta dasa tarihi, kuma ta zama wata alama da ake tunawa da sunan ƙarnin da ta fito. Ta lashe lambobin yabo da dama ciki har da Grammy Awards, kuma ta yi tasirin zama muryar da ba a mantawa da ita a duniyar waƙa da kiɗa.
Babbar jarrabawar da ta fara riskar rayuwar mawaƙiyar ita ce mutuwar mijinta da aka tabbatar suna matuƙar son juna a shekarar 2016, sakamakon cutar daji. Wannan rashin ya girgiza ta matuƙa, saidai a cewarta za ta rayu ko don ‘ya’yanta uku da suka haifa da mijinta.
A yau ‘ya’yan nata ne ke tsaye kanta suna kula da ita kamar yadda ta kula da su kafin girma.
A shekarar 2021, Celine Dion ta bayyana wa duniya halin rashin lafiyar da take ciki, inda ta bayyana ciwon nata a matsayin cutar da ba kasafai take samun mutane ba. Ta kuma yi bayanin yadda cutar ke taɓa mata baiwar waƙa da take da ita, kuma barazanar yiwar ba zata sake iya yin waƙa yadda ta saba ba.
Wannan bayanin ya matuƙar girgiza masoyanta tare da tausaya mata, kuma sun jinjinawa gaskiyar da ta bayyana wadda ke nufin ta ɗauki masoyanta a matsayin wani ɓangare na rayuwarta kamar yadda suka ɗauke ta, kasancewar da yawa a cikin masu shahara sukan ɓoye wasu ɓangarori na rayuwarsu koda masoyansu sun damu da son jin halin da suke ciki.
Mawaƙiya Celine Dion ta zaɓi ta bayyanawa duniya raunin ta, don ya zama wani darasi da zai tunatar da al’umma cewa, duk daraja da shahara ko kuɗin da ka ke da, ba zai hana ka zama ɗan adam ba, kuma shi ɗan adam a kullum yana da rauni.
