Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗaliban za su fara da horon koyon harshen Jamus na tsawon watanni takwas a Abuja kafin su wuce Legas domin rubuta jarabawar cancanta da za ta basu damar ci gaba da karatu a Jamus.
Kwamishinan lafiya na jihar, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana hakan a yayin bikin bankwana da ɗaliban.
Ya ce shirin na daga cikin ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na bunƙasa harkar lafiya da ƙara inganta ƙwarewar ma’aikatan asibitoci a jihar.
Kwamishinan ya buƙaci ɗaliban su zama jakadu nagari na jihar Katsina tare da jajircewa wajen cimma burinsu. “Ku ɗauki wannan dama a matsayin wata hanya ta inganta rayuwarku da ta al’umma baki ɗaya,” in ji shi.
Shi ma shugaban hukumar lafiya a matakin farko Dr. Muhammad Nuradeen Umar ya ce an zaɓo ɗaliban ne daga ƙananan hukumomi 34 na jihar, mutum daya daga kowace ƙaramar hukuma, bisa cancanta da hazaƙar da suka nuna a wuraren aikinsu.
A cewarsa, za a kai ɗaliban wata makaranta mai suna Koode Academy da ke Abuja domin koyon harshen Jamus da kalmomin da ake amfani da su a asibitocin ƙasar.
Dr Muhammad ya bayyana cewa Gwamnati ta samar musu da masauki da kuma alawus na Naira 50,000 duk wata, ba tare da tsayar da albashinsu ba.
Bayan kammala horon harshe, za su wuce Legas domin rubuta jarabawar cancanta a wata cibiyar Jamusawa ta GMBH, inda ake sa ran kowannensu zai samu aƙalla matakin B2 domin samun damar tafiya da ci gaba da karatu a Jamus.
Masana harkokin lafiya na ganin wannan shiri na gwamnatin Raɗɗa babu shakka zai inganta harkokin lafiya a Katsina.
