Bidiyon sanata da Leshaan Dagama: ‘Yar TikTok ta ƙaryata zargin AI da ake yi a bidiyon Adams Oshiomhole

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Fitacciyar ‘yar TikTok kuma mai wallafa hotunan manya daga Afirka ta Kudu, Leshaan Dagama, ta sake tayar da ƙura a kafafen sada zumunta bayan ta fito fili ta ƙaryata iƙirarin da ake yi cewa bidiyon da ya nuna Sanata Adams Oshiomhole a cikin jirgi mai zaman kansa an ƙirƙire shi ne ta hanyar fasahar AI.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani bidiyo ya bazu, inda ake zargin tsohon gwamnan Jihar Edo yana tausa ƙafar wata mata a cikin jirgi. Bayan bidiyon ya bazu, ‘yan Najeriya sun gano matar a matsayin Leshaan Dagama, wadda ta shahara a TikTok da Instagram.

A ranar 4 ga Fabrairu, 2026, ta hannun mai taimaka masa a harkar yaɗa labarai, Sanata Oshiomhole ya musanta bidiyon, yana mai cewa an ƙirƙire shi ne ta hanyar AI. Sai dai Leshaan ta fusata da kalaman, inda ta buƙaci mutane su daina caccakarta, su karkata fushinsu zuwa ga Sanatan.

Ta rubuta a shafinta: “Sanatanku shi ne matsalar. Ku je ku yi fushi da shi, ba ni ba.”

Bayan awanni kaɗan, ta sake girgiza intanet da cewa: “Bidiyon ba AI ba ne, amma ku yarda da Sanatanku.”

Ra’ayoyi sun rabu biyu yayin da kalaman Leshaan suka jawo muhawara mai zafi:

Wasu na ganin tana amfani da lamarin ne domin neman suna, yayin da wasu kuma na zargin sanatan da rashin gaskiya ko kuma mu ce ɓoye gaskiya kan lamarin da ya san ya faru. Wasu sun danganta lamarin da matsalar amana da gaskiya a siyasar Najeriya, a cewar su ba abin mamaki ne ba don babban mutum a siyasar Najeriya ya sharara ƙarya ba.

A ɓangare guda kuwa wasu sun nuna tsoron su kan yadda fasahar AI da deepfake ke iya rikitar da gaskiya a duniya.

Yayin da kowanne ɓangare ke tsaye kan bakar sa, jama’a na ci gaba da sa ido, suna jiran ko za a fitar da hujjoji, karin bayani ko matakin hukuma da zai warware wannan cece-kuce.

Lamarin ya sake tayar da muhawara kan ko irin waɗannan abubuwa za su tilasta wa manyan mutane ɗaukar batun AI da deepfake da muhimmanci a nan gaba.

By ukarofi