
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu rahoton aukuwar gobara a sashen Gidan Glass da ke Kasurwar Singa a Jihar Kano, kusan mako biyu da faruwar irin haka a wani sashen kasuwar.
Shugaban ƙungiyar ‘yan ƙwadagon kasuwar, Hamisu Ɗan Hisbah, a wata hira da manema labarai, ya tabbatar da aukuwar iftila’in a yammacin yau Asabar.
A cewarsa, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar tuni suka garzaya wajen da abin ya faru, inda suka yi ƙoƙarin kashe gobarar, wadda ba a kai ga sanin musabbabin faruwar ta ba.
A lokacin haɗa wannan rahoto, an gano cewa jami’an bada agajin gaggawa suna ƙoƙarin shawo kan al’amarin wajen ganin wutar gobarar ba ta yaɗu zuwa wasu sassan kasuwar ba.
Kusan sati biyu da suka gabata gobara ta kama a yankin Mazaf Plaza na kasuwar, inda ta lanƙwame kayayyakin miliyoyin nairori, lamarin da ya sa ‘yan kasuwa suka fara kokawa game da faruwar gobara akai-akai a yankin.


