
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da iƙirarin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi akansa na alaƙanta shi da ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.
A wata sanarwa daga tsohon kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Kano, Kwamared Muhammad Garba, tsohon shugaban jam’iyyar APCn na ƙasa ya bayyana zargin a matsayin sakaci da rashin gaskiya.
A cewarsa, hakan ƙoƙari ne na karkatar da alhakin wani lamari da ya auku a jihar Kaduna zuaa wani waje da nufin ruɗar da jama’ar ƙasa.
Sanarwar ta jaddada cewa, Dadiyata, wanda sanannen ɗan Soshiyal Mediya ne, yana gudanar da rayuwarsa ne a jihar Kaduna, inda ya shahara wajen yin suka ga gwamnatin jihar.
Ta ƙara da cewa, babu wata hujja da ke nuna cewa ɗan gwagwarmayar ya mayar da hankali ne kan gwamnatin jihar Kano ko Ganduje.
Kazalika, sanarwar ta yi kira da a yi bincike akan kalaman El-Rufai na baya-bayan nan, inda ta jaddada cewa irin waɗannan munanan zarge-zargen su kan zama maganganun siyasa ne kaɗai matuƙar ba a gabatar da wasu ƙwararan hujjoji akansu ba.
