
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta yi sanadin yanke wa sanannen jagoran ‘yan bindiga Ibrahim Usman da aka sani da Ɗan Iyali, hukuncin kisa bisa samun sa da hannu a ayyukan garkuwa da halaka wasu mutum uku a Jihar Sakkwato a watan Satumban 2023.
Rahotanni sun ce, Usman ya fuskanci tuhume-tuhume guda uku ne a Babbar Kotun Adalci ta Jihar Sakkwato da ke sashen shari’a na Sakkwato, tare da wasu da ake nema ruwa-a-jallo. Ababe da aka tuhumce shi da su sun haɗa da makircin aikata miyagun laifuka, garkuwa, kisa da kuma haddasa bala’i acikin al’umma.
Wannan na zuwa ne watanni bayan DSS ta yi sanadiyyar yanke wa wasu mutane uku ciki har da ɗan Nijar hukuncin kisa bisa hannu a ta’addanci da mallakar makamai ba bisa doka ba a Jihar Sakkwato.
Waɗannan mutane sune Yusuf Muhammad da aka sani da Sallau, wanda ɗan Nijar ne; Jabbi Alhaji Yalle; da kuma Kabiru Muhammad, wanda aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya a watan Yunin 2026.
An yanke musu hukuncin ne bayan sashen yaƙi da ta’addanci na DSS ya kama su a Yunin 2025 da hannu a zargin shigowa da makamai daga wata ƙasa da ayyukan ta’addanci.
