Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ranar Assabar ɗin da ta gabata ne aka sami rahoton tsintuwar wata jinjira a Masallacin Shehi Musa Fakkai da ke garin Argungu. Wata darakta a hukumar Hisbah reshen ƙaramar hukumar Argungu Hajiya Rabi Ahmed ta bayyana cewa, Da safiyar Asabar ne suka sami rahoto daga ofis na jami’an tsaro na farin kaya cewa an ga wata jinjira ajiye, saboda haka suka isa wajen suka ɗauki yarinyar kamar yadda aka saba.
Bayan sun ɗauke ta, suka miƙa ta ga wata ƙungiya mai suna Mar’atussaliha da ke da cibiya a Argungu ƙarƙashin jagorancin Hajiya Mariya Mera saboda ta nuna sha’awar riƙe yarinyar.
Ta bayyana cewa gaskiya sun sha samun jinjirai da aka yar amma wannan na musamman ne saboda ba da haifuwar ta aka kawo ta ba aƙalla za ta iya kai sati uku da haihuwar kuma an saka kayan tufafi kamar kala ashirin da kayan kwalliya da man shafi da man kaɗanya da na na alayyadi da sauran abubuwa buƙata wanda yana nuna akwai yiyuwar tsangwama ce ta saka uwar kawo ta nan ta ajiye saboda tunanin za ta shiga hannun ƙwarai saɓanin irin yaran da ake kai jeji waɗansu ko zani babu.
Hajiya Rabi ta ce sai dai duk irin ƙoƙarin da suka yi na neman tallafi daga ƙaramar hukumar Argungu ya ci tura saboda haka suka garzaya fadar mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammed Mera inda aka sami tallafin gaggawa don nemo abubuwan da a ke buƙatar cikin lokaci.
Hajiya Rabi ta ja hankalin iyaye musamman mata da su rinƙa bai wa ‘ya’yan su mata cikakkiyar kulawa don gano irin halin da sukan iya shiga ciki musamman idan irin haka ya faru duk ɗawainiya da ɓacin suna a kan su ya ke sauka.
Ta kuma yi kira ga ma’aikatar mata da ta waiwayo irin waɗannan hukumomin don ba su tallafi musamman na kuɗi saboda ba wata hukuma da ke biyan su albashi ko kuma wani ihsani suna bayar da gudummawa ne ga al’umma kuma hidimar da su ke yi tana buƙatar kuɗi musamman domin sayen magani, sabulu da kayan amfani na yau da kullum ga jinjirai.
