A guji amfani da AI don shigar burtu

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Faifan bidiyo na wani Malamin Bushara da ya ke yayata addininsa ga ‘yan uwansa da ya zayyana da Hausawa Zalla ya bayyana, wannan sam ba laifi ba ne a dokar ƙasa amma laifi ne babba a Baibul don ba inda a ka amince tun daga Littafin FARAWA a Tsohon ALKAWARI har AYYUKAN MANZANNI a sabon ALKAWARI a ka yi bayanin gudanar da wa’azi a doron kabilanci don addini na Allah ne. Don haka mu ke son gaskiyar Zallawa da ke cewa su na da musulmi da Kirista har ma da gargajiya, su nuna kansu riƙe da Baibul a gaban Cocin da su ke sujadar Lahadi.

Abun da ya fito fili Zallawa masu dabarun nuna kan su da dardumar sallah ranar Jumma’a gaban masallaci na amfani da fasahar ARTFICIAL INTELLIGENCE amma ba lallai sun taba kallon gabas a ibada ba. Ba mai kallon gabar na gaskiya da zai karɓi kwangilar zallanci sai dai in ya sha giyar wake.

Kwanan nan wasu daga masu iƙirarin Hausa Zalla su ka yi taro a Kano amma ba su gayyaci ko mai bushara daya tak ba duk da a nan ne a ka yi gagarumin bikin naɗa Sarki Rabaran Shu’aibu Bargi. Mai ya sa sai Sheikh Ibrahim Khalil su ka gayyata shi ma da ya yi jawabi ’yan lakada-kawas su ka yi ta zaginsa? Kazalika sai a gefen taron kuma a ka lakkanawa wani yaro aƙidar wai da Musulmi da Kirista Bahaushe duk ɗaya ne? in daya ne mai ya sa ba a ga Rabaran ko daya ba? Kawai mutanen nan su fito a mutane kowa ya san matsayinsa kawai.

Mu na zuba ido a ranakun Lahadi mu ga shugabannin Zallawa riƙe da Baibul a gaban cocin da su ke sujada sai mu tabbatar da adalci kamar yadda su ke yi wa Musulunci har wani ya daga Alkur’ani ya yi rantsuwa a madadin Zallawa amma bai daga Baibul ba! In ma ba zai iya dagawa ba ai ga mataimakansa nan har ma da ɓoyayyu ‘yan Al-waye-waye. Nan fa wani sarkin ɓuya a ka nuna hotonsa a gaban wata majami’a a Kaduna amma nan ya ce wai majalisar hirarsu ce. Ba wanda ya hana kowa ’yancin yin addininsa da harkarsa amma an haramta shigar burtu kuma an haramta AIFOB.

In da ba ƙasa a ke gardamar kokawa. Hujja kawai ba yakin sunkuru ba.

Duk yadda za ka yi kokarin sakaya batun zallawa, ƙarshe don mugun halinsu, sai ka fito da hotonsu na yaƙi da Musulunci kuma ba sa bin koyarwar addinin Kirista.

Watannin baya ai yadda Zallawa ke magana ta girmama GIJI da gizagizai da Gijimasu wadanda duk abubuwan bautar Maguzawa ne; sai mu ke ganin ai tafiyar ta jikokin Maguzawa ne da ke son farfaɗo da addininsu. Zallawa sun so cin gajiyar sunan Maguzawa don hakan ka iya ba su damar alaƙanta kansu da Hausawa. Fitowa da mu ka yi mu ka nuna Hausawa daban Maguzawa daban ya sa su sauya dabara. Kai in ka na maganar Hausawa fa Musulunci sak ka ke magana!

Maimakon mu ga Zallawa watarana yadda su kan je taruka a Makoda ko wani gari da wani yaro mai murguɗaɗɗen baki ya kira da Gurumbawa, su ziyarci Maguzawa a Sumaila ko Rogo; sai kwatsam mu ka ga su na nadawa wani rawani wai shi ne sarkin Hausawa kirista na Kano don an yi gori wai Bahaushe ba zai iya mulkin kansa ba! Shin wa ya taɓa cewa Bahaushe ba zai iya mulkin kansa ba? Yanzu ma uwar wa ke mulkin? Wannan izgilanci ne ga Hausawa.

Wallahi nan na kawo mu ku yadda wani Bazalle mai karyar ASABIYYA ya yi rubutu ya na girmama Barbushe inda ya rubuta “Maigida Barbushe..” don neman alaƙanta Zallawa da Barbushe daga nan sai su zalle da cewa su ne asalin mazauna Kano! A gaskiya za su yi shari’a da Barbushe a kiyama, ba abun da ya haɗa Barbushe da sakarcin nan na Midibelawa/AIFOB. In sun yi musu, mai ya sa kwanan nan da wasu Zallawa su ka yi majalisi a Kano ba su hau Dutsen Dala ba don ayyukan ibada ko mutunta tarihi? Mai ya sa su ka shiga gidan Malam Aminu Kano MAMBAYYA su ka ce MUNBAYYA ne?.

Tun da zallawa sun nada Sarkin Hausawa Kirista na Kano, to ina sarkin Musulmi Hausawa na Kano?

Mun zuba ido tsawon watanni har ma shekara bayan ganin naɗin Sarkin Kirista Hausawa na Kano da HAUSA CHRISTIAN DEɓELOPMENT INITIATIɓE ta yi, amma ba mu ga na Sarkin Hausawa musulmi zalla ba. Shin ko dai mabiya addinin Kirista ne ke kishin Bahaushe ya mulki kansa su kuma sauran na mara mu su baya? Kai jama’a fa da hankalinsu ragas kuma kar su ke kallon take-taken mutanen nan masu ɓoye kan su da yaɗa sharri ta shigar burtu a yanar gizo.

Tuni su ka zayyana Sarkin Kano da Sarkin Fulani da furta miyagun kalamai duk da ba inda a ka taɓa naɗa wani sarki da sunan na ƙabila kuma hatta wani faifan na sarkin Kano da su ke sakawa a ziyarar da ya kai wa Shehun Borno ya nuna shi Bafulatani ne bai ce Fulani ya ke yi wa sarauta ba. Yo Kano har Ibo da Yarbawa a ke da su waɗanda kuma a nan a ka haife su. Ba ma su kaɗai ba akwai Larabawa daga Yaman da Lebanon da Kanawa ne kuma duk sarkin ke sarautarsu. Shin ba Barebari ne a Kano ko ba Jukunawa a Kano?

Abun da ya bayyana a zahiri mabiya addinin Kirista ke da himmar wannan aiki na Hausa Zalla tun da sun fito karara sun bayyana kan su. Ba ma ta batun sarauta ba har ma da shiga cikin ƙauyuka su na bayanin su Hausa Zalla ne kuma mabiya addinin Kirista. Duk da dai ba inda a ka ba da hurumi a Baibul wani ya dinga tsalle da ware ƙabilarsa wai ya na mu su wa’azi. Shi addinin Kirista na duk wanda ya yi ban gaskiya ne don samun fadar sama “Littafin Matta sura ta 7 aya ta 7” kowa zai iya kwankwasawa a buɗe ma sa ba wani zalla ko mai haɗi ko ma waye.

Tun da kullum aikin shi ne zagin Shehu Mujaddadi, malaman Musulunci da manyan sarakuna, duk wanda ya nazarci tafiyar zai gane su waye ke gudanar da ita. Idan har mabiya addinin Kirista Hausawa za su iya naɗa Sarki kuma su ne marar sa rinjaye a tsakanin Hausawa, ina Musulmin Zallawa su ke ba su nada Sarkin Hausawa musulmi Zalla ba?.

Kun ga kamar yadda na rubuta a baya, idan yaudara ne sai su mannewa Musulunci kamar wurgo hotunan AI ranar Jumma’a wai don a ce su Musulmi ne amma sam ba za ka ga sun yi hakan a ranar Lahadi wajen sujada a coci ba. Mutanen da su ke cewa su na da Musulmi da Kirista har ma mun ga sarkin da su ka naɗa amma sai shigar burtu.

Har dai maganar Hausa ta gaskiya a ke yi, dole ne Zallawa su fara naɗa Sarkin Hausawa Musulmi gabanin na kirista da su ka yi. KO DAI DUK KIRISTOCI NE ZALLAWAN? A tsarin mulkin Nijeriya an ba wa kowa hurumin shiga addinin da ya amince da shi amma ba a amince mutum ya buya bayan addini don tada fitina ta wutar ƙaiƙayi ba.

Na ga wani sabon salo da Zallawa ke yayatawa da taimakon manhajar AI cewa ‘yan ta’adda su ke son a murkushe “BANDITS MUST GO” maimakon yadda su ka share tsawon lokaci su na ruruta kiyayyar ƙabilanci don haɗa Musulmi yaƙi musamman daga masallatai a shiga dauki ba daɗi a doron ƙabilanci a madadin sahu ɗaya da tuta ɗaya ta Musulunci. Wallahi da tun farko wannan hanya su ka bi kusan kowa zai zama Bazallen yaƙi da ‘yan ta’adda!.

Abun da ke nuna min ba lallai da gaske su ke yi ba shi ne ba su ba wa al’ummar Arewa haƙuri da yadda su ka yi ta cin mutuncin malaman addini da shugabannin siyasa na tun jamhuriya ta farko irin su firmiya Sir Ahmadu Bello su ka ɗauki maciyin amana Chukwuma Nzeogwu a matsayin gwarzonsu. Hakanan masu cewa su na marawa ballewar Biyafara daga Nijeriya da kururuta cewa ƙabila ta fi addini kuma abun da ya fi zama hatsari shi ne zayyana koyarwar Shehu Mujaddadi da cewa shi ne yanzu ɓarayin daji ke yi!? Daga jin wannan ka san waɗanda za su iya ambata haka mutanen ne kura da fatar akuya.

KAMMALAWA

Tun da sun sauya manufa a zahiri don ba mu san badini ba, to sai su haɗa kai da jami’an tsaro da sauran hukumomi don ceto Arewa daga wannan mummunan yanayi da ke jawo asarar rayuka da dukiya. Ya zama ba zagin kowa a wajen tarukansu kuma su haramtawa duk mai ɓoye kansa da sunan karya da shafin bogi shiga sabgarsu. Da zarar boyayye ya yi magana su yi watsi da shi. Shin za su iya? Ai yaƙi da miyagu ba sai mutum ya buya ruffff a salula ba in dai shi din ba Kob da Rob ba ne Danjuma da Danjummai da miyagun irin.

Wani muhimmin abu shi ne su nesanta tafiyarsu da ’yan AIFOB gama ai ba makiya Nijeriya lamba ta daya irin AIFOB. Duk mai hulɗa da AIFOB ai kai tsaye ya kama zama mai cin amanar ƙasa. Mu ga sun riƙa shiga shafukan AIFOB su na gargaɗinsu da hawainiyarsu ta kiyayi ramar Hausa da Hausawa.

By ukarofi

Leave a Reply