Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su kawo ƙarshen dogaro da fitar da albarkatun ma’adinan ƙasa zuwa ƙasashen waje ba tare da samun cikakkiyar fa’ida daga sarrafa su, bunƙasa masana’antu da ƙera kayayyaki daga gare su ba.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin da yake wakiltar Shugaban ƙasa Bola Tinubu a taron manyan jami’ai na uku na Africa Minerals Strategy Group (AMSG) da aka gudanar a New York. Ya ce, Afirka ba za ta iya ɗaukar kanta a matsayin nahiya mai arziki ba, alhali kuwa al’ummomin da ke zaune a yankunan da ake samun ma’adinai na ci gaba da rayuwa cikin talauci.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya kuma yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka, yana mai gargaɗin cewa bai kamata ƙasashen nahiyar su rika gogayya wajen jawo masu zuba jari ta hanyar rage kuɗaɗen sarauta da ake karɓa daga ma’adinai, raunana ƙa’idojin amfani da kayayyakin cikin gida da kuma bayar da rangwame fiye da kima ba.
Maimakon haka, ya ba da shawarar samar da haɗaɗɗun kasuwanni, cibiyoyin sarrafa ma’adinai na shiyyoyi da kuma hanyoyin jigilar ma’adinai tsakanin ƙasashe, domin bai wa Afirka damar cin gajiyar yawan albarkatunta da kuma ƙarfafa matsayinta a tsarin samar da ma’adinai na duniya.
Shettima ya bayyana wasu sauye-sauyen da Nijeriya ke aiwatarwa a fannin ma’adinai, ciki har da ƙara mayar da hankali kan ƙara darajar ma’adinai a cikin gida, inganta bayanan binciken ƙasa, shigar da masu haƙar ma’adinai ƙanana cikin tsarin doka, da kuma ɗaukar matakan yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Ya kuma yi nuni da ƙaruwa da aka samu a kuɗaɗen shiga daga fannin ma’adinai da kuma zuba jari da ake yi wajen sarrafa lithium a Jihar Nasarawa, yana mai cewa waɗannan na daga cikin damar da ke akwai wajen ƙara amfana da ma’adinai a cikin gida.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya nuna goyon bayansa ga Tsarin Ci Gaban Tabbatacce ga Kowa (Mutual Assured Development – MADE Framework) na AMSG, yana mai cewa dole ne gwamnatoci su samar da manufofi tabbatattu da hukumomi masu inganci, yayin da masu zuba jari kuma ya kamata su kawo jari mai ɗauke da alhaki, fasahar zamani, ƙara darajar kayayyakin cikin gida da kuma ɗorewar jajircewa wajen zuba jari.
Ya kuma yi kira da Sanarwar Haɗin Kan Nahiyar da Tabbatar da Tattalin Arziki (Continental Integration and Economic Assurance Declaration) ta wuce matakin sanya hannu kawai, ta koma shirin aiwatarwa mai ɗauke da ƙayyadaddun lokutan aiwatarwa, hanyoyin samar da kuɗaɗe da kuma tsarin ɗaukar alhaki.
Shettima ya ce a ƙarshe, nasarar dabarun Afirka na bunƙasa fannin ma’adinai ya kamata ta bayyana a cikin samar da tituna, layukan dogo, masana’antu, kamfanonin Afirka masu gogayya a kasuwannin duniya, ayyukan yi masu buƙatar ƙwarewa da kuma bunƙasar al’ummomin da ke zaune a yankunan haƙar ma’adinai. Ya jaddada cewa mallakar albarkatun ma’adinai kaɗai ba ta isa ta tabbatar da wadata ba.
A nasa ɓangaren, Ministan Bunƙasa Ma’adinai Masu Daraja, wanda kuma shi ne Shugaban AMSG, Dele Alake, ya gabatar da shawarar kafa Asusun Afirka na Shigar da Masu Haƙar Ma’adinai ƙanana Cikin Tsari da Kare Lafiyarsu. Ministan ya ce, ya yi imanin cewa irin wannan tsari zai taimaka wajen rage yawan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, wadda ya ce ta haddasa mutuwar sama da mutane 200 a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a watan Janairu, ta kuma yi sanadin mutuwar ɗaruruwan masu haƙar ma’adinai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a watan Agusta, yayin da wasu 60 suka mutu a West Kordofan na Sudan kwanaki kaɗan da suka gabata, sakamakon rugujewar wuraren haƙar ma’adinai.
Alake ya ce, irin wannan tsari zai iya taimaka wa ƙasashe mambobin ƙungiyar wajen hanzarta kafa ƙungiyoyin masu haƙar ma’adinai da ba su lasisi, samar da bayanan binciken ƙasa na asali, samun ingantattun kayan aiki masu aminci, horas da ma’aikata kan lafiya da tsaron wurin aiki, farfaɗo da muhalli da kuma, musamman, shirye-shiryen tunkarar gaggawa a manyan wuraren haƙar ma’adinai na gargajiya.
Taron ya samu halartar ministocin ma’adinai na ƙasashen Afirka mambobin ƙungiyar, hukumomin samar da kuɗaɗen raya ƙasa, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da manyan jami’an kamfanonin ma’adinai, fasaha da sarrafa ma’adinai.
Haka kuma, wakilin Gwamnatin Amurka kuma Mai Ba Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Shawara ta Musamman kan Ofishin Harkokin Afirka, Chris Kulukundis, ya halarci taron, inda ya bayyana aniyar gwamnatin Amurka ta yin haɗin gwiwa da Afirka wajen amfani da albarkatun ma’adinan nahiyar.
ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a taron shi ne sanya hannu da ƙasashe mambobin ƙungiyar suka yi kan wata yarjejeniya mai suna Sanarwar Haɗin Kan Nahiyar da Tabbatar da Tattalin Arziki.
Ana sa ran sanarwar za ta samar da sabon tsarin haɗin gwiwar ƙasashen Afirka wajen kula da muhimman ma’adinai, ciki har da ƙara darajar ma’adinai ta hanyar sarrafa su a nahiyar da kuma daidaita manufofi tsakanin ƙasashe.
