INEC ta sanar da fara bada katin zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da ranar 9 ga Oktoba, 2026 a matsayin kwanan watan fara bayarwa da karɓar katin zaɓe (PVC) yayin cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya sanar da haka a ranar Litinin a Kaduna yayin ganawa da jami’an hukumar na shiyyar Arewa maso Yamma da jaddada shirinta na gudanar da zaɓen na 2027.

Amupitan ya ce, aikin karɓar katin shi ne mataki na uku daga cikin matakan rajistar masu zaɓe, wanda ya samar da sababbin masu rajista guda 10,772,421, waɗanda suke dakon tantancewa ta na’ura, wato Automated Biometric Identification System.

Ya kuma umarci jami’an hukumar da su tabbatar da warware matsalolin da ke haifar da giɓi ga ayyukansu da kuma toshe dukkan wata hanya da ka iya dakatar da waɗanda suka yi rajista samun katinansu musamman jama’ar karkara.

A cewarsa, zagayen da suke yi a shiyyoyin Nijeriya shida yana da nufin gano matsalolin da ake fuskanta a fagen ayyukansu da kuma samar musu da mafita gabanin babban zaɓen ta yadda al’umma za su gamsu da ƙoƙarinsu wajen tabbatar da yin adalci a fannin.

Farfesan ya ƙara da cewa, akwai buƙatar a yi adalci da nuna ƙwarewa acikin jami’an INEC, sannan yadda suke gudanar da lamuran ƙananan hukumomi, cibiyoyin rajista da rumfunan zaɓe sune abin da jama’a za su kalla wajen yarda da su ko akasin haka.

By Babaji

Leave a Reply