
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Asabar ne Majalisar Wakilai ta ce za ta yi zaman gaggawa a ranar Talata 17 ga watan Fabrairu, 2026, domin duba batutuwan da suka taso a game da fitar da jaddawalin zaɓen 2027 da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi a jiya Juma’a.
Sanarwar, wadda mai magana da yawun majalisar, Hon. Akin Rotimi ya fitar ta bayyana cewa an sanar da mambobin ne ta wata takarda ta cikin gida da ofishin shugaban majalisar ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
Ta jaddada cewa zaman gaggawar ya nuna ƙudurin majalisar na ɗaukar matakin daidaita al’amuran da ke da matuƙar tasiri ga tsarin dimokraɗiyyar Nijeriya.
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi sanarwar INEC, daidai da ayyukan majalisa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
INEC ta sanar da cewa, za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar jiha a ranar 6 ga watan Maris, 2027.
Sai dai kuma wasu ‘yan Nijeriya musamman musulmi sun nuna damuwa kan ranar da za a gudanar da babban zaɓen ƙasar, inda suka yi nuni da cewar ya zo ne a cikin watan Ramadan.
