Kotu ta yi watsi da buƙatar bada izinin binciken shaidar NYSC na Ministan Cikin Gida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a wata Babbar Kotun Tarayya da ke a birnin Tarayya Abuja ta hannun Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta ƙi amince wa buƙatar ɗan gwagwarmaya Emorioloye Owolemi ta a duba sahihancin takardar kammala hidimar ƙasa (NYSC) ta Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Buƙatar, wadda aka ƙi karɓar, ta nemi a ba ta damar tantance takardar NYSCn ministan, wanda ya yi ikirarin karɓar ta a shekarar 2006.

Owolemi ya kuma nemi kotun ta tilasta wa ministan ya gabatar da takardun da ke tabbatar da halascin kuɗaɗen alawus da aka biya ma’aikata a ƙarƙashinsa da waɗanda aka biya na wasu ayyuka ta bankuna tare da gamsassun bayanai akan su da kuma halin zargin barin ofishin da aka ce ministan ya yi.

Da yake hukunci, Mai Shari’a Abdulmalik ya ce ƙorafin bai cika sharuɗɗan ‘yancin samun bayanai ba, dom haka ya yi watsi da shi.

A wani labarin kuwa, wata Babbar Kotun Tarayya da ke a Abuja ta amince da buƙatar ƙorafin da aka shigar mata da ke neman ta bayar da izinin a yi bincike akan sahihancin takardun karatun Tunji-Ojo.

Mai Shari’a Binta Nyako a ranar Juma’a ta amince da hakan a takardar da Owolemi ya gabatar domin neman gano sahihancin takardar kammala sakandarensa ta WAEC.

Lauyan ɗan gwagwarmayar, Philemon Yakubi (SAN) ya miƙa takardar bisa hukuncin dokar ‘yancin samun bayanai sashe na 1, 20 da na 21 a kundin 2011.

A yayin hukuncin, Alƙalin ta ba lauyan izinin cigaba da gudanar da binciken gano ainihin sahihancin shaidar WAEC ɗin ministan..

Daga nan ne mai shari’ar ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Maris

By Babaji