Daga AISHA ASAS
A cikin ‘yan shekaruna nan an samu sauyi mai girma a yadda mata musamman masu harkar fim ke kallon matsayin jikinsu da fata. Tagomashin dirin jikin mace da kuma hasken fata sun zama ababen mafi tattaunawa a kafafen sada zumunta. Maza da yawa na yaba mata masu hasken fata da kuma diri, wataƙila hakan ne ke sa mata fita hayyacinsu wurin neman mallakar waɗannan abubuwa ido rufe.
A can baya, mata kan dogara da ababen jiƙo ko kayan magunguna don ƙara girman mazaunai ko nono, ko kuma samun hasken fata, waɗanda akasari ba su cutarwa saidai su ƙi aiki.
Saidai mata na wannan zamani sun ce hakan bai ishe su ba, sun fi son sha yanzu magani yanzu, wanda hakan ya sa likitoci a ɓangaren suka bazama neman yadda za su samar masu da biyan buƙata, wanda wannan ne ya ƙyanƙyashe BBL da kuma bilis.
Shafin Taurari na wannan mako zai zufafa kan ma’anar waɗannan hanyoyi na ƙarin halitta, yadda ake aiwatar da su, abinda masana suka faɗa kansu, da kuma uwa uba dalilin da ya sa suka fi yawaita a tsakanin jaruman fim, wanda a nan ne alƙalaminmu zai fi karkata.
Da farko dai shin mene ne BBL?
BBL wato Brazilian Butt Lift, hanya ce ta tiyatar gyara ko ƙarin sassan jiki, wadda ake fassarawa da ɗagawa ko ƙara girman bayan mace ta hanyar amfani da kitse na jikin mutum.
Likitocin gyaran jiki sun bayyana yadda ake wannan sauyin halittar wadda suka ce ana yin ta ta matakai uku:
Fitar da kitse(Liposuction): Wannan mataki na farko zai ciro kitse daga wasu sassa na jiki kamar ciki, ƙugu, cinya da makamantan wuraren da kitse ke iya taruwa.
Tace kitse: Sun bayyana mataki na biyu a matsayin tace kitsen don cire masa jini ko wata datti da take tattare da shi.
Saka kitse a inda ake so: Matakin ƙarseh kuwa za a kai kitsen ne a inda ake buƙatar ƙara girman wato mazaunai ko hifs domin cika aikin na girman ko “inganta” siffa.
Duk da cewa amon bayanin yadda ake yin shi zai zama tamakar abu mai sauƙi ko marar illa duba da cewa wani sashe ne aka cire aka ƙara wa wani sashe. Wasu ma kan ce ai akan yi hakan a wasu curuta, kamar idan mutum ya samu ƙaton ƙurci da sai an yanke shi, wani lokacin girman ko irin ciwon da ya haddasa shi kan buƙaci a ɗebo wata tsoka a masa dashe don cike giɓin da cewon ya bari. Hakan ke sa mata da yawa kan ruɗe kansu kan cewa babu laifi ko illa ga aikata hakan, dalilin kenan da ya kawo yawaitar masu yin wannan tiyata, kamar yadda binciken ƙungiyar likitocin gyaran jiki ta Amurka ta fitar cewa, BBL na daga cikin tiyatar kwalliya da aka fi yawaita yi a duniya a cikin shekarun baya-bayan nan, hakan kuwa ya samu ne sakamakon yadda al’umma ke sha’awar sifar jiki mai ƙugu da baya mai faɗi.
Idan mun fahimci abin da kyau, bari mu koma kan tambayar ko yin hakan na da hatsari ga lafiyar wadda ta yi?
Masana kiwon lafiya sun yi gargaɗin cewa, duk da kasancewar BBL hanyar gyaran ciki da aka amince da ita a asibitoci, tana da haɗarin gaske idan ba a yi sa’a ba.
Daga cikin ababen da suka ambata za su iya samuwa ta sanadiyyar wannan tiyata akwai zubar jini mai yawa da zai iya zama barazana ga rayuwa baki ɗaya. Kamuwa da wasu curuta waɗanda a can baya mai jikin ba ta taɓa fuskanta ba. Dasƙarewar jini a jijiyoyi, da kuma matsalar numfashi idan kitse ya shiga cikin jini. Wani lokacin kuwa akan samu rashin sa’a idan aikin ya zo da ƙiyawa sai wurin ya lalace yana wari har ma ga wasu yana fitar da tsutsa, kamar dai yadda ya faru ga wata jarumar Nollywood a ‘yan shekarun baya-bayan nan.
Idan mun fahimci BBL bari mu koma kan fassarar ma’anar bilis:
Bilis kalma ce da aka saba amfani da ita wajen fassara bilicin, wato sauya launin fata ta hanyar rage kaurin launin fata (melanin) ta hanyar amfani da sinadarai ko allurai.
Ana yin sauyin fata ta hanyoyi da dama, daga ciki akwai;
Man shafawa: Ana amfani da man da ke ɗauke da sinadarai kamar hydroƙuinone, corticosyeroids ko mercury.
Allura: Wasu na zaɓar canza launin fatarsu ta amafani da allura da aka ƙirƙira musamman don irin wannan aikin.
Tiyatar hasken fata (laser): Wani lokacin ana amfani da wata na’ura mai haske domin rage duhun fata, ko ince haskaka fata ta ƙarfin tuwo.
Bilis bai kasance abu da ya kamata duk wani mai hanakli ya yi ba, ba wai a iya addini ba har ma wasu ƙungiyoyin lafiya sun yi gargaɗi kan hakan, duk da cewa su ba hanawa suka yi ba kamar yadda addini ya rahamta ba, sun dai sanar da hatsarin da ke cikin yin kauɗi kan halittar Allah a kaikaice, inda suka nuna akwai hatsarin gaske idan aka yi amfani da mayukan da ba su da inganci, inda suka ce za a iya haɗuwa da illoli kamar haka; lalacewar fata har ta zama abin ƙyama, kamuwa da wasu curuta na fata ciki kuwa har da kansar fata, lalacewar ƙoda ko hanta, kamuwa da curuta sakamakon raunana garkuwar jiki.
Kamar yadda masana suka bayyana, fata tana da kariya da Allah ya halitta mata, kuma duk wani yunƙuri na sauya ta ta hanyar da ba ta dace ba na iya jawo mummunan sakamako.
Idan mun gane shimfiɗar da muka yi, za mu je kan ɓangaren da ya shafi wannan shafi, wato shin me ya sa BBL da bilis suka fi yawaita a tsakanin jaruman fim?
Masana’antar fim wuri ne da za mu iya cewa ababen da ake buƙata daga mata don zama jarumai suka ninka na maza nesa ba kusa ba. Daga cikin abanen da ake duba ga mace akwai siffar jikinta ko launin fatarta, wanda ba kasafai suke zama manyan ababen duba ba ga jarumi namiji ba matuƙar ya iya aktin sosai.
Blueprint Manhaja ta tattaro wasu dalilai da ke sa wasu da yawa a masa’anatar fim shiga waɗannan ɗabi’u masu hatsarin gaske.
1. Matsin lambar samarwa ‘yan kallo buƙatarsu:
Rayuwar jarumai idan ta fara shahara kamaninsu da kwalliyarsu takan kuɓecewa buƙatunsu ya kai ba su da iko kan yadda jikinsu zai kasance ko yanayin fatarsu. Rayuwarsu gaba ɗaya za ta koma ta masu ɗaukarsu fim, su kuma masu fim ɗin suna duba ga buƙatun masu kallo ne waɗanda da bazarsu suke taka rawa.
Za mu iya cewa babu masana’anatar fim a duniya da ba ta kallon kyaun mace a matsayin manyan dalilan saka ta fim, wanda sau da yawa masu ƙarancin kyau suke samun matsala a yawan saka su a fina-finai.
Sau da dama idan aka fitar da neman jaruma, kalmar fara da kuma mai diri yana yawan shawagi a cikin ababen da ake so ta mallaka, wannan kuwa na tunzuwa wasu matan zuwa ga neman hanyar da za su mallaki ababen da ake buƙata ta kowace hanya.
2. Kafafen sada zumunta:
Wasu za su yi mamakin sanyo kafafen sada zumunta cikin wannan layin, saidai da taimakon bayanin da zan yi yanzu za a fahimci inda na dosa. Kafafen sada zumunta ta zama duniya ta biyu da mutane ke shaƙar numfashi a cikinta, kuma hanya ce da aka fi jin ra’ayoyin jama’a da kuma samun karɓuwar fina-finan da ake yi. Abin nufi, fim na tasiri ne idan al’umma sun gamsu da shi, ana sanin gamsurar fim a wannan zamani ta hanyar kafafren sada zumunci. Wannan ya sa jarumai da waɗanda ke neman sharaha ke mayar da kafafen sada zumunci iyayensu wurin biyayya, ta hanyar yawan yaɗa hotunansu don neman yawaba da soyayyar mabiya, wanda hakan zai sa ga jarumai kamfanonin fina-finai su yi ribibinsu. Su kuma masu neman shahara su samu biyan buƙatar da suka yi domin ta.
Shi ya sa za ku ga musamman ma a mata, suna damuwa da ababen da ‘yan kwament suke faɗa kan jiki ko wankansu, a cewar wasu ita ce kasuwarsu. Sau dayawa za ka tarar wani ma yaro ne ƙarami zai aibata wani ɓangare na jikin wata, sai ya samu magoya baya da yawa, kamar misali a faɗi yadda jaruma ta ƙara ƙiba, kuma ƙibar ba ta yi mata kyau ba, zai iya zama dalilin da ita da masu kula da ayyukan sana’ar tata su yanke shawarar ta nemi hanyar rage ƙibar. Wannan na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ka ke jin wasu jarumai musamman na ƙasashen ƙetare suna ƙorafin rashin damar cin abinda suke ra’ayin ci, sakamakon kula da jikin da masu aiki da su ke yi. Wani lokacin ma har ɗaukar masana ake yi da za su dinga kula da irin abincin da jaruman ke ci, a ƙoƙarin ganin ba ta yi ƙibar da ba a so ta yi ba, ko cin wani abu da zai taɓa kyan fatarta ko makamantansu.
Za mu cugaba a mako mai zuwa da yardar Allah.
