Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da Umarnin Zartarwa na 9 na shekarar 2026, wanda ya tanadi cewa dukkan kuɗaɗen shiga daga harkokin man fetur su riƙa shiga kai tsaye zuwa Asusun Kwamitin Raba Kuɗin Tarayya (FAAC).
Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya yi bayani kan muhimman matsayi da aka cimma a taron kwamitin aiwatar da umarnin.
Matakin ya biyo bayan umarnin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na cewa a riƙa mayar da dukkan kuɗaɗen man fetur da suka shafi tarayya zuwa asusun FAAC, tare da ƙaddamar da kwamitin da zai kula da aiwatar da dokar.
A cewar Ministan, kwamitin ya sake jaddada umarnin Shugaban ƙasa cewa dukkan kuɗaɗen da ke shigowa tarayya daga ayyukan man fetur dole ne a tafiyar da su bisa tanadin kundin tsarin mulki, tare da kare haƙƙin matakai uku na gwamnati – tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Sanarwar ta ce, bisa ga umarnin, kamfanin NNPC zai dakatar nan take da karɓar kaso 30 cikin 100 na kuzin gudanarwa da kuma kaso 30 cikin 100 na asusun binciken sabbin rijiyoyin mai (frontier eɗploration fund) daga ribar mai da iskar gas ƙarƙashin kwangilolin rabon samarwa (Production Sharing Contracts).
Haka kuma, za a dakatar da tura kuɗaɗen tara na ƙone iskar gas zuwa Asusun Ginshiƙan Gas na Tsakiya da ƙasa (MDGIF) har sai an kammala sabbin tsare-tsare.
Dangane da sashe na 2(3) na umarnin, wanda ya tanadi cewa ‘yan kwangila su riƙa biyan kuɗaɗen kai tsaye cikin asusun tarayya, Ministan ya bayyana cewa kwamitin ya amince da samar da wani zangon sauyi, domin tabbatar da cewa sabbin matakan ba su karya yarjejeniyoyi ko tsarin kuɗaɗe da aka riga aka ƙulla ba, tare da kiyaye kwarin gwiwar masu zuba jari.
Ya ce har sai kwamitin ya fitar da cikakkun ƙa’idoji, ‘yan kwangila za su ci gaba da biyan kuɗaze bisa tsarin da ake amfani da shi a yanzu. A lokacin zangon sauyin, za a samar da cikakkun jagorori na bai ɗaya domin tabbatar da sauyin ya gudana cikin tsari da gaskiya.
Ministan ya ƙara da cewa, an amince da kafa ƙaramin kwamitin fasaha wanda zai tsara cikakkun jagororin sauyin cikin makonni uku, tare da fara duba Dokar Masana’antar Man Fetur domin gyara duk wasu giɓin tsari da na kuɗi da ke shafar kuɗaɗen tarayya. Za a jagoranci wannan ƙaramin kwamitin ne daga ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Makamashi, tare da haɗin gwiwar Babban Lauyan Tarayya kuma Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Shari’a, Shugaban Hukumar Haraji ta ƙasa da kuma Shugaban ƙungiyar Kwamishinonin Kuɗi na Jihohi.
A ƙarshe, Ministan ya yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai da goyon baya, yana mai cewa manufar wannan gyara ita ce tabbatar da cewa albarkatun man fetur na Nijeriya sun samar da anfani kai tsaye ga al’ummar ƙasa baki ɗaya.
