Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa Yankin Kasuwanci na Musamman (Free Trade Zone) mai faɗin hekta 4,000 a Jihar Kogi, a wani mataki da ake ganin zai buɗe sabuwar babi wajen farfazo da masana’antu da kuma cika burin sake tayar da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta da ya daɗe yana tangal-tangal.
Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin karcar takardar lasisin sabuwar Ajaokuta Free Trade Zone daga hannun Hukumar Kula da Yankunan Sarrafa Kayayyakin Fitarwa ta Nijeriya (NEPZA).
Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin tsalle zuwa sahun gaba na bunƙasar masana’antu, yana mai danganta amincewar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar tun watan Nuwamban shekarar da ta gabata a matsayin ginshiƙin wannan nasara.
A cewarsa, sabon yankin kasuwancin zai buɗe ƙofar zuba jari daga ƙasashen waje da kuma na cikin gida, tare da ƙarfafa ƙoƙarin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta, kamfanin ƙarafa da ya shafe shekaru yana durƙushe.
Ya ƙara da cewa, Kogi jiha ce ta musamman wadda ke makwabtaka da jihohi har goma da kuma Babban Birnin Tarayya, tare da arzikin ma’adanai sama da 30 ciki har da zinariya, tama ta ƙarafa, lithium da beryllium. Sai dai ya nuna cewa waɗannan albarkatu ba su amfanar da jama’a yadda ya kamata ba a baya.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar samar da tsaro, ingantattun ababen more rayuwa da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa domin jawo hankalin masu zuba jari. Ya bayyana cewa takardar shaidar da aka miƙa musu wata alama ce ta buɗe ƙofar kasuwanci ga duniya, tare da jaddada cewa kafin ƙarshen shekarar nan ana sa ran Ajaokuta za ta fara aiki yadda ya kamata.
Yayin da yake mayar da martani kan damuwar da ake da ita dangane da gazawar yunƙurin da aka taɓa yi na farfaɗo da kamfanin a baya, gwamnan ya nuna kwarin gwiwa cewa wannan karo gwamnati za ta yi nasara, musamman ganin sabon tsarin da aka tsara wanda ya haɗa da Yankin Kasuwanci na Musamman domin ƙarfafa ɗorewar tattalin arziki.
A nasa ɓangaren, Babban Daraktan NEPZA, Dakta Olufemi Ogunyemi, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na zaukar matakai masu tsauri wajen farfaɗo da yankunan kasuwanci da suka daɗe ba su aiki a fadin ƙasar nan. Ya ce duk lokacin da Shugaban ƙasa ya ayyana yankin kasuwanci na musamman, yana tare da alhakin samar da ayyukan yi, musayar fasaha da ci gaban al’umma.
Ya bayyana cewa idan yankin kasuwanci bai yi aiki ba, to ba ya samar da aikin yi ko musayar fasaha, kuma hakan asara ce ga ƙasa. Ya ambaci ƙoƙarin sake farfaɗo da yankuna kamar Tinapa a Jihar Kuros Riba da wasu a Jigawa da Borno, yana mai cewa matsalolin kuɗi, rashin tsaro da raunin tsarin kasuwanci su ne suka haddasa gazawarsu a baya.
Ogunyemi ya jaddada cewa tsarin yankunan kasuwanci na musamman wata dabara ce ta duniya wadda ke jawo masana’antu, sarrafa kayayyaki da ayyukan hidima, tare da jawo jarin ƙasashen waje da hada tattalin arzikin cikin gida da na waje ta hanyar samar da sarkar kayayyaki.
Matakin kafa Yankin Kasuwanci na Ajaokuta na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin sake fasalta tattalin arzikin ƙasa, tare da mayar da hankali kan masana’antu da samar da ayyukan yi, abin da masana ke ganin zai iya zama muhimmin tubali wajen ciyar da Nijeriya gaba.
