Hukumar NDIC ta bayyana yadda ake biyan masu ajiya a bankunan da suka rushe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Inshorar Ajiya ta Nijeriya (NDIC), Oludare Sunday, ya yi cikakken bayani kan yadda hukumar ke biyan masu ajiya a bankunan da suka gaza tare da shiga matakin rushewa, yana mai jaddada cewa akwai iyaka da doka ta gindaya wajen biyan kuɗaɗen.

Ya bayyana hakan ne a lokacin zaman kare kasafin kuzin shekarar 2026 a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Inshora da Ilimin Kimiyyar Lissafin Haɗari, wato ‘Actual Matters’, wanda ya gudana a Abuja.

A yayin zaman, Mai Magaba da Yawun Majalisar Wakilai kuma mamba a kwamitin, Honarabul Akin Rotimi Jr, ya nemi ƙarin haske kan yadda ake sasanta masu ajiya da bankunan da suka rushe, musamman kan adadin da kowane mai ajiya ke da haƙƙin karɓa.

Da yake amsa tambayar, Shugaban Daraktan NDIC ya ce ɗaya daga cikin manyan ayyukan da doka ta ɗora wa hukumar shi ne bayar da tabbacin kariya ga ajiya. Ya ce domin aiwatar da wannan aiki, NDIC na karɓar wani kaso na kuɗin inshora, wato premium, daga bankuna bisa ajiyar da suke riƙe da shi, kuma ana lissafa wannan kaso ne bisa kimanta haɗarin da kowace cibiyar kuɗi ke fuskanta.

A cewarsa, “Ba duk kuɗin ajiyar da bankuna ke karɓa ba ne muke karɓa a matsayin premium. Abin da muke karɓa ƙasa da kashi ɗaya cikin ɗari ne. A baya yana kusan kashi 15 bisa 16 na cikin ɗari. Don haka, kariyar ajiyar da muke bayarwa tana dogara ne a kan wannan tsari.”

Ya ƙara da cewa, aikin NDIC ya bambanta da na sauran kamfanonin karɓar ajiya kamar kamfanonin inshora, domin a nan banki ne ke biyan premium, ba mai ajiya ba. Mai ajiya ne ke amfana idan rikici ya taso, domin NDIC na tabbatar da cewa an gudanar da bankuna yadda ya kamata tare da tsare muradun jama’a.

Oludare Sunday ya bayyana cewa adadin da doka ta tabbatar a matsayin kariya shi ne naira miliyan 5 ga bankunan kasuwanci, bankunan ajiyar jama’a,wato Deposit Money Banks, bankunan lamuni na gidaje, wato Primary Mortgage Banks, da kuma kamfanonin hada-hadar kuɗi ta zamani, wato Mobile Money Operators. Amma ga sauran cibiyoyin kuɗi, iyakar kariyar ita ce naira miliyan 2.

Shugaban kwamitin, Honarabul Ahmed Jaha, ya yaba da bayanin da Shugaban Daraktan ya yi, yana mai cewa akwai buƙatar wayar da kan jama’a kan cewa NDIC ba ta rufe dukkan adadin ajiyar da mutum ya yi ba, domin akwai iyaka da aka ƙayyade a doka.

Bayani na NDIC ya sake jaddada muhimmancin fahimtar tsarin inshorar ajiya a Nijeriya, musamman a lokacin da ake fuskantar sauye-sauye a bangaren banki, domin tabbatar da kwanciyar hankali da amincewar jama’a ga tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasa.

By ukarofi