Karancin gas ya janyo raguwar lantarki zuwa megawat 4,300 – NISO

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Tsarin Lantarki ta ƙasa (NISO), ta danganta raguwar samar da wutar lantarki a faɗin Nijeriya da matsalar ƙarancin iskar gas da kuma takurawar ƙarfin samar da wuta daga tashoshin samarwa.

A cikin wata sanarwa da mahukuntan ɓangaren gudanar da tsarin wutar suka fitar a ranar Juma’a, sun bayyana cewa matsalolin biyu sun haddasa faɗuwar matsakaicin wutar da ake iya samarwa zuwa megawatt 4,300 kacal.

Hukumar ta ce, mafi yawan tashoshin samar da wutar lantarki na tururi (thermal plants) ba su iya aiki yadda ya kamata ba sakamakon rashin wadataccen gas.

Sanarwar ta yi ƙarin haske da cewa tashoshin thermal su ne ke riƙe da kaso mafi girma a tsarin samar da wutar lantarki na ƙasa, don haka duk wata tangarɗa a samar da gas kai tsaye na rage yawan wutar da ake iya tura wa kasa baki ɗaya. 

Sakamakon haka, adadin wutar da ake rabawa Kamfanonin Rarraba Wuta (DisCos) ya yi ƙasa da yadda aka saba.

Bayanan aiki da aka tattara sun nuna cewa tashoshin thermal suna buƙatar kimanin miliyan 1,629.75 na cubic feet na gas a kowace rana domin su yi aiki yadda ya kamata. Sai dai zuwa ranar 23 ga Fabrairu, 2026, adadin gas da aka samu ya tsaya ne a kimanin miliyan 692.00 na cubic feet a rana, abin da ke nuni da babban giɓi a buƙata da samarwa.

Hukumar ta bayyana cewa wannan adadin bai wuce kashi 43 cikin 100 na abin da ake buƙata ba, lamarin da ya takaita yawan wutar da ake iya samarwa da kuma rabawa ga masu amfani da ita. A cewarta, wannan shi ne babban dalilin da ya sa aka rage rabon wutar ga kamfanonin rarrabawa.

Dangane da matakan da ake ɗauka, NISO ta ce idan jimillar wutar da ake samarwa ta yi ƙasa sosai, dole ne a aiwatar da tsarin yanke wuta a wasu sassa domin daidaita lodi, tare da rarraba adadin wutar da ake da ita bisa tsarin kaso-kaso da NERC ta gindaya a ƙarƙashin tsarin MYTO, domin tabbatar da daidaiton cibiyar sadarwar wuta da kauce wa rushewar tsarin gaba ɗaya.

Hukumar ta nuna nadama kan irin wahalar da wannan hali zai jefa masu amfani da wutar lantarki da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwar wutar lantarki, amma ta tabbatar da cewa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomi da masu samar da gas domin ganin an dawo da cikakken rabon wuta da zarar an inganta samar da gas da ƙarfin tashoshin samarwa.

By ukarofi