Haɗa fim da wata sana’a ce mafita ga ‘yan fim don guje wa ɓacin rana – Musa Maisana’a 

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

Fitaccen jarumi a masana’antar finafinai ta Kannywood Musa Abdullahi wanda aka fi sani da Musa Maisana’a, ya yi kira ga masu gudanar da harkokin su a masana’antar da su rungumi wasu sana’o’in da kasuwanci kada su tsaya a fim kaɗai. 

Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da yadda masana’antar take a yanzu inda yake cewa 

“A yanzu ko siyasa kake yi to ka haɗa da wata sana’ar, duk abin da ka san za ka samu ɗari da kwabo ka yi, kada ka dogara da fim kaɗai. Domin idan ka dogara da fim kaɗai, zamani ne, kuma lokaci ne, don haka idan kai ne yau ba kai ne gobe ba. Da can ba mu ba ne wasu ne. Saboda haka idan ka samu dama ka yi amfani da damar ka, idan mace ce ko da kosai ne kunu ne shinkafa ce mayafai da turaruka duk ki yi kada ki ga wai ke ‘yar fim ce kin wuce ki yi sana’a. To duk Annabawa babu wanda bai yi kasuwanci ba, domin hakan ne zai sai duk juyin da harkar fim ta yi, to ba za ta yi maka barin lyaunwa ba.”

Dangane da fitowar sa a cikin finafinai kuwa Maisana’a ya ce ” Har yanzu ina fitowa, ko in ce a yanzu ne ma nake fitowa. Don kuwa duk wanda yake hawa YouTube Channels zai ga Maisana’a Kano TV a nan zai rinƙa kallon finafinai na, irin su ‘Kunnen Kashi’, ‘Malamin Mata’, ‘Ke Magajiya ya ne ‘Kukan Marayu’. Yanzu haka kuma ina da fim ɗin ‘Matar Soja’ yana nan, kuma duk ranar Litinin ina haska ‘Maiunguwa Kasaci’ da sauran finafinai. 

Baya ga haka har na jama’a ina yi, duk wanda yake da buƙatar na fito a fim ɗin sa zai gayyace ni, idan na faɗa masa tsari na ya amince zan je na yi masa. Amma dai a yanzu iya nawa ɗin ma sai a hankali, saboda hidimar da take gaba na. Domin bayan fim ina sana’a da yawa har sayar da motoci, don haka harkoki na sai godiyar Allah, kuma ina godiya ga jama’a saboda yaba mana da suke yi da kuma bibiyar mu. Ina yi wa kowa fatan alheri.”

By ukarofi