Nishadi

Ina matuƙar kishin masana’antar Kannywood – Mu’azzam Idi Yari 

Ina matuƙar kishin masana’antar Kannywood – Mu’azzam Idi Yari 

(Ci gaba daga makon jiya) Daga MUKHTAR YAKUBU  A daidai lokacin da aka samu sauyin shugabanci a tashar talabijin ta ALGAITA TV wadda take haska finafinan Hausa na masana'antar Kannywood bayan saukar shugaban ta na farko Umar Sani Kofar Mazugal inda aka maye gurbin sa da sabon shugaba Mu'azzam Idi Yari. A yanzu haka an samu wasu canje-canje da kuma ci gaban tashar domin tafiyar da ita daidai da bukatar al'umma. Kan haka ne wakilinmu ya tattauna da sabon shugaban Mu'azzam Idi Yari domin bayyanawa masu karatu inda alkiblar ALGAITA TV ta sa a gaba, don haka sai ku biyo…
Read More
Duk wani abu da za mu yi na gina KILAF AWARD tare da ‘yan Kannywood mun yi, amma kamar ba su shirya amsar sa ba ne – Muhammad Galadima

Duk wani abu da za mu yi na gina KILAF AWARD tare da ‘yan Kannywood mun yi, amma kamar ba su shirya amsar sa ba ne – Muhammad Galadima

Daga MUKHTAR YAKUBU  Taron bikin bajekolin finafinai na Afirka wato 'Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festiɓal' wanda aka saba gudanar da shi a garin Kano a duk shekara, wanda a bana zai kasance shi ne karo na 9 tun daga lokacin da aka fara shiryawa. Babu shakka wannan taron ya kasance taro na farko da ake shiryawa a masana'antar finafinai ta Kannywood da ya shafe tsawon shekaru ana gudanar da shi ba tare da ya tsaya ba.  Kuma wannan wani abin alfahari ne da Kamfanin Moɓie Image bisa jagorancin Malam Abdulkarim Muhammad ya samar ga ci gaban…
Read More
Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  *Ba a amince da allurar glutathione don sauya launin fata ba - Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka An samu rahotannin mace-mace da suka danganci BBL fiye da wasu hanyoyin gyaran jiki - ASERF Mercury na iya haddasa lalacewar ƙoda, matsalar jijiyoyin jiki da kuma illa ga jarirai idan mai ciki na amfani da shi - WHO  2. Kafafen sada zumunta: Wasu za su yi mamakin sanyo kafafen sada zumunta cikin wannan layin, saidai da taimakon bayanin da zan yi yanzu za a fahimci inda na dosa. Kafafen sada…
Read More
Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

Matsin lamba ko son rai: Yadda BBL da bilicin suka zama al’ada a masana’antun nishaɗi

Daga AISHA ASAS A cikin 'yan shekaruna nan an samu sauyi mai girma a yadda mata musamman masu harkar fim ke kallon matsayin jikinsu da fata. Tagomashin dirin jikin mace da kuma hasken fata sun zama ababen mafi tattaunawa a kafafen sada zumunta. Maza da yawa na yaba mata masu hasken fata da kuma diri, wataƙila hakan ne ke sa mata fita hayyacinsu wurin neman mallakar waɗannan abubuwa ido rufe. A can baya, mata kan dogara da ababen jiƙo ko kayan magunguna don ƙara girman mazaunai ko nono, ko kuma samun hasken fata, waɗanda akasari ba su cutarwa saidai su…
Read More
Idan asusuna ya yi ƙasa da miliyan N200 Ina shiga matsi, inji hadimin Davido

Idan asusuna ya yi ƙasa da miliyan N200 Ina shiga matsi, inji hadimin Davido

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani mataimaki ga fitaccen mawaƙin Nijeriya Davido, mai suna Dre, ya janyo zazzafar muhawara a kafafen sada zumunta bayan ya bayyana adadin kuɗin da yake ɗauka a matsayin “talauci” a rayuwarsa. A wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, Dre — wanda ake dangantawa da tawagar DMW — ya ce idan ya buɗe asusunsa ya ga ƙasa da Naira miliyan 200, zai ɗauki kansa a matsayin wanda ya shiga matsin kuɗi. A cikin salon magana na Pidgin, ya ce: “If like N200 million remain for my account, I go dey feel like say I…
Read More
Yadda Masana’antar Kannywood ke alhinin rasuwar Nura Shariff 

Yadda Masana’antar Kannywood ke alhinin rasuwar Nura Shariff 

Daga AISHA ASAS  *Gidauniyar Kannywood ta yi jimamin rasuwar sa *An rufe ofishin Abnur da ke Kano har zuwa kammala addu’ar kwanaki 7 *Arewa Cultural Group ta yi alhinin rasuwar Nura Shariff *ABNUR da masu ruwa da tsaki sun dakatar da ayyuka don girmama marigayin Masana’antar fina-finai ta Kannywood ta shiga cikin babban alhini yayin da gidauniyar Kannywood da ƙungiyoyi daban-daban suka bayyana kaɗuwar su tare da alhini game da rasuwar tsohon jarumi kuma ƙwararren manajan shirye-shirye, Nura Shariff. Marigayin ya shahara wajen aiki a kamfanin Abdul Amart na ABNUR Entertainment, inda ya taka rawar gani a shirya fina-finai da…
Read More
Eric Dane: Duniya ta girgiza da rashin jarumin ‘Grey’s Anatomy’ Dr. Mark Sloan

Eric Dane: Duniya ta girgiza da rashin jarumin ‘Grey’s Anatomy’ Dr. Mark Sloan

 Daga AISHA ASAS  A ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairu, 2026, duniya ta yi rashin Eric Dane, ɗan wasan kwaikwayo da ya shahara sosai musamman a rawar da ya taka a cikin shahararren shirin talabijin na likitanci mai suna Grey’s Anatomy, inda ya yi fice a matsayin Dr. Mark Sloan, wanda masoya suka fi sani da laƙabin McSteamy. Dane ya rasu yana da shekaru 53, bayan doguwar gwagwarmaya da cutar amyotrophic lateral sclerosis (ALS), wadda aka fi sani da Lou Gehrig’s disease, cuta mai haddasa lalacewar jijiyoyin da ke sarrafa tsokoki kuma ba ta da magani a likitance. Dane ya…
Read More
An kammala zangon farko na ɗaukar fim ɗin ‘Five Winners’  

An kammala zangon farko na ɗaukar fim ɗin ‘Five Winners’  

Daga MUKHTAR YAKUBU  A yanzu haka dai an kammala zangon farko na ɗaukar wani gawurtaccen fim mai dogon zango wanda Kamfanin Jammaje Production ya ɗauki nauyin shiryawa inda aka shafe kusan kwanaki ashirin ana gudanar da aikin. Fim ɗin mai suna 'Five Winners' dai tun kafin fara aikin sai da aka yi masa shiri na musamman ganin yadda aikin fim ɗin zai ɗauki tsawon lokaci da kuma maƙudan kuɗaɗe. A tsawon kwanakin da aka yi dai ana aikin abubuwa sun faru da dama wanda hakan ya mayar da fim ɗin na daban a cikin ayyukan fim da aka daɗe ba…
Read More
Haɗa fim da wata sana’a ce mafita ga ‘yan fim don guje wa ɓacin rana – Musa Maisana’a 

Haɗa fim da wata sana’a ce mafita ga ‘yan fim don guje wa ɓacin rana – Musa Maisana’a 

Daga MUKHTAR YAKUBU  Fitaccen jarumi a masana'antar finafinai ta Kannywood Musa Abdullahi wanda aka fi sani da Musa Maisana'a, ya yi kira ga masu gudanar da harkokin su a masana'antar da su rungumi wasu sana'o'in da kasuwanci kada su tsaya a fim kaɗai.  Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da yadda masana'antar take a yanzu inda yake cewa  "A yanzu ko siyasa kake yi to ka haɗa da wata sana'ar, duk abin da ka san za ka samu ɗari da kwabo ka yi, kada ka dogara da fim kaɗai. Domin idan ka dogara…
Read More
Waƙa: Bishiyar Zumunci

Waƙa: Bishiyar Zumunci

Daga MOHAMMED BALA GARBA  1. Rabbana ka ji ƙan zumunci,            Don a yau mun ruguza shi. 2. Babu mai duba gare shi,               Ko ya ce zai ɗabbaka shi. 3. Ga shi Allah yai bayani,               Kansa domin mu riƙe shi. 4. Ya yi alƙawari na narko,        Gun waɗanda suke katse shi. 5. ɗaha ya yi kira gare mu,                A Hadisai don mu yo shi. 6. Ya faɗo falalar zumunci,                       Da azaba in ka ƙi shi. 7. Yau idan ka tsaya ka duba,                    Duka ba ma aikata shi. 8. Mun yi watsi da zumunci,              Babu mai neman a yo shi. 9. Har…
Read More