Ali Nuhu ya yi wa Tinubu godiya kan naɗin da ya yi masa

Daga BASHIR ISAH

Jarumi a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Ali Nuhu, ya mika godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Tinubu kan nadin da ya yi masa a gwamnatinsa.

A wannan makon mai karewa ne Tinubu ya nada jarumin a matsayin Shugaban Hukumar Fina-finai ta Kasa tare da wasu a karkashi Ma’aikatar Al’adu ta Tarayya

A ranar Juma’a Ali Nuhu ya wallafa sakon godiyar a shafinsa na facebook inda ya ce, “Godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu wa ta’ala, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Salallahu alaihi wa sallam.

*Ina mika sakon godiyata ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da Mataimakim Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Shugaban Jam’iyya APC na Kasa, Umar Ganduje.

“Ministan Al’adu Hon Hannatu Musawa a kan wannan matsayi na Manajin Darakta na Hukumar Fina-finai ta kasa.

“Ina godiya ga abokan sana’ata, yan’uwa da abokan arziki daukacin magoya bayana da suka taya ni murna da adduo’i. Allah ya ba mu ikon daukar nauyin da ya rataya a wuyanmu don wannan mukamin namu ne gaba daya. Ya kuma bamu ikon fita kunya.”

Samun wannan mukami da jarumin ya yi bai zo da mamaki ba, musamman idan aka yi la’akari da rawar da yake takwa a masana’antar shirya finafinai na cikin gida.