Shekara 70 da kafa GTC: Ƙungiyar KANTOBA ta yi rawar gani – Salisu Dala

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

An bayyana cewa ƙungiyar tsoffin ɗalibai ta makarantar fasaha ta Kano wato Kano Government Technical College GTC ta yi rawar gani musamman ganin yadda aka ɗauki kwanaki uku ana hidimar bikin cika shekara 70 da kafuwar makaranta GTC wacce aka kafa a shekarar 1952 yadda a ranar farko ɗalibai suka taru aka yi addu’a da sauke Ƙur’ani domin ci gaban makaranta da yin addu’ar ga wanda ya kafa makarantar mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero dama sauran wadanda suka taimakawa makarantar daga Shugabannin ta da malaman ta har zuwa yau dinnan.

sai kuma ranar ta biyu da aka yi kaddamar da asusun neman taimako don saya wa makarantar wasu kayayyakin koyarwa domin amfanin daliban makarantar na yanzu a matsayin gudummawa daga wannan Kungiya KANTOBA, wanda aka tara kudi kimanin miliyan biyu.

Sai kuma ranar ta uku wanda aka qaddamar da jarida ta bayanai akan wannan makaranta da kuma kungiyar tsoffafin daliban ta KANTOBA wannan abin yabo ne sosai ga shugabancin wannan kungiya a wannan lokaci, kamar dai yadda shugaban makarantar na yanzu Malam Adamu Salisu Dala ya bayyana a wannan lokaci.

Haka kuma ya yaba wa manyan baki kamar sarakuna da shugabanni da babban sakatare kuma shugaban hukumar kula da makarantu kimiyya da fasaha na Kano ES Farfesa Dahiru Sale wanda shi ma tsohon dalibi ne a GTC shekaru 27 da suka wuce da sauran manyan baki da shugannin wannan kungiya da suka bada gudunmawa da hadin kai dan ci gaban wannnan makaranta.

A qarshe shi ma Farfesa Dahiru Sale ya bayyana cewa wannan gwamnati ta zo da kyakywan kuduri wajen daga darajar makarantun kimiyya da fasaha na Kano ta hanyar gyara su da sabunta su kamar dai yadda wannan gwamnati ta kuduri inganta harkar ilimi da ci gaban Kano ta kowanne fanni na rayuwar al’ummar Kano.