Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da sanarwar rage yawan jami’an da za su rika yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai je ciki da wajen kasar.
Matakin ya shafi dukkan ministoci da manyan jami’an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban kasa da uwargidan shugaban kasa.
Sanarwar wadda Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban Nijeriya kan harkar yada labarai ya fitar ranar Talata na cewa matakin, wani yunkuri ne na rage yawan kudaden da jami’an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye.
Ta ce yawan jami’an da za su rika yi wa shugaban kasa rakiya zuwa kasashen waje, nan gaba ba za su wuce jami’ai 20 ba.
Haka zalika, Ngelale ya ce Tinubu ya ba da umarnin a daina tura dumbin jami’an tsaro zuwa wata jiha a duk lokacin da zai kai ziyara can, maimakon haka za a rika amfani da jami’an tsaron da ke jihar ne kawai don tabbatar da tsaro.
