Da Ɗumi-ɗumi: Babbar Kotu ta hana ci gaba da sauraren ƙarar da aka shigar kan mawaƙi Rarara bisa zargin sukar Buhari

Daga BASHIR ISAH

Wata Babbar Kotun Jihar Nasarawa da ke zamanta a yankin Doma ta dakatar da Kotun Majastare ta 1 da ke Lafia daga ci gaba da sauraren ƙarar da wani matashi mai suna Sani Ahmad Zangina ya shigar kan fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara, bisa zarginsa da sukar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari.

Lauyan da ke jagorantar tawagar lauyoyin Rarara, Barrister A. I Ma’aji, ya bayyana wa manema labarai cewar sun ɗaukaka ƙara a gaban Mai Shari’a Abdullahi H. Shamsu Shama na Babbar Kotu da ke Doma tun ranar Litinin ta ƙarshen watan jiya, bisa rashin gamsuwa da umarnin Kotun Majastare da ta tilasta lallai dole Rarara ya bayyana a gabanta.

Sai dai lauyan wanda ya shigar da ƙarar, Barista Isah Hassan Nalaraba, ya ce ba su da masaniyar ɗaukaka ƙarar da lauyoyin mawaƙin suka yi, abin da kawai ya sani shi ne, akwai zaman kotun ranar juma’a.

Idan za a iya tunawa, Kotun Majastare da ke Lafia ta sanya ayyana Juma’a, 2 ga watan Fabrairun 2024 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraren ƙarar.

Yanzu dai jama’ar da ke bibiyar wannan batu da ma ‘yan jarida na hanƙoron yadda za ta kasance a kotun ya zuwa ranar Juma’a, 2 ga Fabrairun da ake ciki.