Saudiyya ta yi wa Nijeriya ragin kudin aikin Hajjin 2024

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Alhazan ta Kasa (NAHCON) ta sanar da cewa Saudiyya ta yi wa Nijeriya ragin kudin aikin Hajjin bana don samun saukin wadanda za su tafi aikin Hajjin bana daga kasar.

NAHCON ta ce shugabanta, Jalal Ahmad Arabi ne ya mika bukatar neman ragin domin walwalar mahajjatan Nijeriya.

Bayanin haka na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun NACHON, Fatima Sanda Usara, ta fita a ranar Laraba, inda ta ce ragin ya shafin kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake yi wa alhazai yayin aikin Hajji a Saudiyya.

Sanarwar ta ce biyo bayan bukatar neman ragin da NAHCON ta gabatar wa Saudiyya, kasar ta amince ta rage wa Nijeriya Dala 138 daga kudin tikitin jirgin da aka biya yayin Hajjin 2023. Sannan masauki a Madina da aka saba biyan Riyal 2,080 ya koma 1,665, yayin da  masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.

A cewar snarwar, “Alal misali, an samu ragin kudin masauki a Madinah daga Riyal 2,080 kamar yadda aka biya a 2023  zuwa Riyal 1,665 a bana.

“Sannan a Makkah an rage kudin masauki zuwa Riyal 3000 sabanin Riyal 3,500 da aka biya bara.

“Mahajjatan 2024 Riyal 4,770 za su biya a matsayin kudin Masha’ir (hadi da haraji) sabanin Riyal 5,393 da aka biya a bara.

“Game da kudin tikitin jirgi kuwa, NAHCON ta samu nasarar sama wa maniyyatan Nijeriya ragin $138 daga farashin da aka biya bara.”