Rura wutar rikici a Filato ba alheri ba ne

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A daidai lokacin da nake wannan rubutu mazauna Karamar Hukumar Mangu a Jihar Filato na zaune a gidajensu cikin cikin fargaba da takura, sakamakon dokar ta baci na tsawon awa 24 da gwamnatin jihar ta kafa, domin hana bazuwar rikicin da ya varke tsakanin matasan kabilar Mwaghavul da Hausawa da Fulani. Kodayake har kawo yanzu ba a gama kididdige yawan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi ba, amma daga bayanan da ke fitowa daga wasu mazauna yankin an salwantar da rayuka da dukiyoyi masu yawa, musamman a rana ta biyu da rikicin ya cigaba da bazuwa.

Bisa ga nazarin abubuwan da ke faruwa, akwai kwakkwarar shaidar da ke nuna rikicin na da nasaba da kabilanci da addini, domin kamar yadda mazauna jihar ke bayyanawa, garin Mangu na daga cikin yankunan Filato da ya yi suna kan zaman lafiya, saboda yadda iyalai da ‘yan uwa da suka fito daga bangaren Musulmi da Kirista suke cudanya da juna, ba tare da nuna wariya ba. Duk tsawon shekarun da aka yi ana rikici a Jihar Filato yankin Karamar Hukumar Mangu ya kasance cikin zaman lumana, in ban da ’yan kananan fitintinu na nan da can. Dalilan da ake dangantawa da gambizar zamantakewar mutane yankin, sakamakon kasancewar Mangu gari ne da kusan kowanne iyali ake samun Musulmi da Kirista da suka fito daga tsatso daya.

Tun bayan hare-haren jajiberen Kirsimeti da aka kai kan wasu kauyuka da ke Kananan Hukumomin VBokkos, Mangu da Barikin Ladi inda aka yi asarar rayuka fiye da dari, yankin shiyyar tsakiyar Filato da wani sashi na arewacin jihar ya shiga rudani, da zaman dar-dar, sakamakon fargabar da ake da ita ta yiwuwar kai harin ramuwar gayya da kisan mummuke, ko yawaitar zargin juna da zai cigaba. Shi ya sa ake ganin rikicin baya-bayan nan na Karamar Hukumar Mangu cigaba ne daga kashe-kashen da suka afku a jajiberen Kirsimeti. Lura da yadda kuskure kadan ya jawo asarar wasu karin rayuka da dama.

A zantawar da ya yi da tashar BBC Hausa, wani shugaban matasan kabilar Mwaghavul ya shaidar da cewa, ana zargin wasu matasan Fulani ne suka jefi wasu matasan Mwaghavul da ke tafiya a kan babur wanda hakan ya haifar musu da raunuka, har suka jefar da baburansu suka ruga wajen jami’an tsaro domin kai rahoton gaggawa, yayin da suka kira ‘yan uwansu da ke gida suka shaida musu abin da ke faruwa.

Daga wannan jawabi za a fahimci idan dai har wannan shi ne dalili to, bai kai a ce an samu asarar rayuka da muhallan jama’a masu dimbin yawa ba, sai dai idan dama akwai wata jikakkiya a kasa. Domin kamar yadda shugaban matasan ya yi zargi babu tabbacin su wanene suka yi jifan, da aka ce shi ya hassala rikicin, sai dai hasashen yaran Fulani ne kawai. Yayin da su kuma Fulanin suka yi zargin ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, suna wuraren kasuwancinsu a cikin gari suka ga ana far musu da muhallansu, har ma da wuraren ibada.

Sai dai an rahoton na daban an rawaito cewa, lamarin ya auku ne a kan hanyar Jos zuwa Mangu, inda wani dan kabilar Mwaghavul daga yankin Sabon Gari ya buge wata saniya da ke kiwo da babur dinsa, yayin da shi kuma Bafulatanin da ke kiwon saniyar ya kai masa duka da sanda. Daga nan kuma rikici ya kaure, har dai jami’an tsaro suka shiga tsakani don sasantawa.

Ko ma dai wanene ya tsokano wannan fitina mun ga yadda rashin hakuri da rashin bin ka’ida wajen neman hakkin wani a wurin jami’an tsaro da hukumomi, suka haifar da salwantar rayukan da har yanzu ba a gama iyakance su ba. Yayin da rayuwa ke kara kunci da tagayyara masu karamin karfi, mata da ƙananan yara, wadanda wannan fitinar ba za ta amfanar da su da komai ba, musamman cikin yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa.

A cewar wani mazaunin garin Mangu, barnar da aka yi a tsawon awoyi 48 din da ake wannan rikici, garin ya yi lalacewar da za a jima bai dawo cikin hayyacinsa ba. Saboda iyalai sun tarwatse, ’yan uwa na jini daya sun halaka ’yan uwansu, sakamakon dadaddiyar adawa da kiyayyar da ta dade tana cin wasun su a rai.

Savanin sauran rikice-rikice da suke aukuwa a yankin da ake yawan dangantawa da rikicin makiyaya da manoma, wannan fitinar ta Mangu a cewar wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya fi kama da fadan addini, domin a cewarsa, rikicin bai tava ofishin wata jam’iyyar siyasa ko wata majami’a ba, sai dai an kona masallatai da makarantun Islamiyya, an kuma kona unguwanni biyu na Musulmi da akasarinsu ‘yan kabilar Mwaghavul ne.

Jaridar Premium Times ta rawaito wani mazaunin yankin Mangu Halle na shaidar da cewa wasu matasa masu dauke da makamai a rana ta biyu sun shiga yankin Gangaren Kwata da sanyin safiya suna neman inda aka voye Fulani don su kashe su, daga bisani kuma kashe-kashe da kone-kone suka cigaba da watsuwa ana kona masallatai da wuraren kasuwanci.

Wannan fitina ta rikicin kabilanci da addini da ke neman dawowa Jihar Filato ba alheri ba ce ga jihar da al’ummarta, sakamakon yadda a baya jihar ta yi ta fama da koma-baya da rashin cigaba, a dalilin rikice-rikicen da suka rika aukuwa kusan shekaru fiye da 20. Kudaden da gwamnati ke warewa don gudanar da aikace-aikacen cigaban kasa, an rika karkatar da su wajen kula da harkokin tsaro da samar da tallafi ga ’yan gudun hijira, da sauran bukatu na tsaro. Yayin harkokin kasuwanci suka rushe aka daina samun shigar baki ‘yan kasuwa cikin jihar saboda tsoron rayukansu da dukiyoyinsu.

Yanzu da ake murnar an samu dawowar zaman lafiya da farfadowar kasuwanci da walwalar jama’a, abin kunya ne da takaici a ce an bai wa wasu tsiraru masu muguwar aniya damar sake mayar da hannun agogo baya a jihar. Musamman ma a yanzu da sabuwar gwamnati da ba ta dade da samun amincewar Kotun Qoli a matsayin halastacciya kuma zababbiyar gwamnati, karkashin Gwamna Caleb Mutfwang dan kabilar Mwaghavul ke kokarin daidaita zamanta ba.

Ya kamata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, shugabannin rundunonin tsaro, da Gwamnatin Jihar Filato su tashi tsaye su tabbatar da ganin cewa, ba a koma gidan jiya a jihar ba. Sannan kuma ba a cigaba da asarar rayuka da dukiyoyin jama’a ba.

A kuma tabbatar da an gano masu hannu wajen kunna wutar rikici a lokaci irin wannan, a hukunta su don su zama abin misali ga sauran da ke da niyyar amfani da kalubalen tsaro a jihar wajen arzuta kansu da cimma wasu muradunsu na siyasa ko na son zuciya.