Abin takaici ne yadda ake samun hannun mata a almundahana – Jamila Tijjani 

“Taɓarɓarewar tarbiyya daga gida ke samo asali”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Gimbiyarmu ta wannan mako ba kowa ba ce illa Hajiya Jamila Tijjani Abdullahi, tsohuwar lauya, tsohuwar ma’aikaciyar banki, tsohuwar jami’ar gwamnati, malamar makaranta, ƴar kasuwa, kuma mai kishin cigaban rayuwar mata da matasa, kuma shugabar kungiyar Jam’iyyar Matan Arewa a Jihar Filato. ‘Ya ce a wajen fitaccen dan siyasar nan na Arewa kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar Switzerland, Ambasada Yahaya Kwande.

Har-wa-yau, mijinta Alhaji Tijjani Abdullahi, mai lakabi da George Best, tsohon dan siyasa ne kuma babban dan kasuwa a cikin garin Jos. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Gimbiyar tamu ta bayyana burin da ta dade da shi a ranta na yi wa jama’a hidima da kuma takaicinta na yadda aikin banki ke fuskantar koma baya a kasar nan. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

HAJIYA JAMILA: To, kamar yadda aka sani sunana Jamila Tijjani Abdullahi, kuma babbar ƴa a wajen Alhaji Yahaya Kwande, basarake, tsohon jami’in gwamnati wanda ya yi aiki tun zamanin tsohon Firimiyan Arewa Sardaunan Sokoto, Sa. Ahmadu Bello. Tsohon dan siyasa kuma dan kasuwa a nan Jihar Filato. Ni tsohuwar ma’aikaciyar banki ce, kwararriya a harkar kula da shige-da-ficen kudi, kuma ƴar kasuwa, uwa kuma kaka. Ina auren Alhaji Tijjani Abdullahi, muna da yara biyar biyu mata uku maza. Ina kuma da jikoki uku. 

Ki gaya mana tarihin rayuwarki a takaice.

Ni haifafiyar garin Jos ce. Amma na yi makarantar firamare a Capital School Kaduna, wacce a lokacin makaranta ce da aka warewa yaran ma’aikatan gwamnatin Arewa a lokacin, ana kai mu daga Jos. Bayan na kammala a shekarar 1975 sai na samu damar shiga makarantar hadaka ta ƴammata a Queen’s Elizabeth School da ke Ilorin a Jihar Kwara a lokacin ina cikin yara mata 5 da suka cancanci shiga makarantar daga nan Arewa. Na kammala a shekarar 1980.

Na wuce karatu zuwa makarantar share fagen shiga Jami’a a Zariya 1981zuwa 1982, inda gwamnatin farar hula ta wancan lokacin ta tura babana, Alhaji Yahaya Kwande don ya zama Jakadan Najeriya a Switzerland, don haka sai muka bi shi can. Daga bisani ya samar mana makaranta ni da kannaina a Ingila, a wata makarantar gaba da sakandire da ake ce wa Woodhouse Grove School a yankin Yorkshire da ke arewacin Ingila.

Bayan na gama mun dawo gida, sai na sake neman cigaba da karatu a Jami’ar Jos, inda na karanci aikin lauya. Bayan na gama sai na tafi Makarantar Horar da Lauyoyi da ke Legas. Sannan na dawo Jos na yi aikin Hidimar kasa a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Filato. Bayan na kammala ne sai na samu aiki a bankin Habib wanda yanzu ya koma Keystone, inda na yi aiki a Kaduna na tsawon shekara 6, kafin daga baya aka yi min canjin wajen aiki zuwa Jos. Daga bisani na bar aikin banki, saboda dalilai na dawainiyar gida.

Na koma aiki tare da Ma’aikatar Ruwa ta Jihar Filato, inda na yi aiki har tsawon shekara 16 har na kai matakin Mataimakiyar Darakta. Sai kuma na zo na ajiye aiki, don mayar da hankali wajen kula da makarantar da maigidana ya bude Trust International School, wanda dama take karkashin kulawata. Muna da sashin rainon yara na Nursery, akwai sashin firamare, da sakandire. Wannan shi ne aikin da har yanzu nake kai.

Sai dai kuma a bangaren karatu na yi karatun digirina na uku a Jami’ar Jos, inda na karanta ilimin sasanta rikice-rikice da, samar da zaman lafiya, na kuma yi diploma ta musamman a vangaren gudanarwa.

Yaya ki ka kalli kalubalen da mata masu iyali ke fuskanta a bangaren aikin banki, duba ga lokacin da ki ka yi naki aikin?

Na fara aiki a bankin Habib ban yi aure ba, sai daga baya. Daga nan ne na fara fuskantar kalubale, saboda ga hidimar gida ga ta ofis, kuma a lokacin har na fara samun girma na zama ofisa mai kula da ma’ajiyar kudi. Ni ce mai fitar da kudi da mayarwa, bayan an tashi a aiki, wani lokaci har karfe goman dare muna kai wa a banki, har sai an daidaita alkaluman lissafi sun tafi daidai.

A lokacin komai da hannu ake yi, babu na’ura kamar ta yanzu da aikin ya yi sauki. A gida kuma ba ni ce kadai mata a wajen mijina ba, ina da kishiyoyi. Don haka duk ranar girkina, sai an makara a girki, saboda ba na komawa gida da wuri, duk da kasancewar ina da masu taya ni aikace-aikace. Sai bayan na haifi yarinyata ta biyu ne, ni da kaina na zauna na yi nazarin matsalolin tafiyar da aiki da gudanar da harkokin iyalina na ga gaskiya takurar ta yi yawa, ya kamata in ajiye aikin haka. 

Kin samu wata damuwa ne da maigidanki, na rashin samun lokacinki a gida? 

Sam, ko kadan bai nuna min wata damuwa ko rashin jin dadi ba. Abin ma ya zama masa abin alfahari ne cewa matarsa na aikin banki, wanda a lokacin aiki ne mai martaba sosai. Mutane na girmama mu, ana mana kallon masu amana da gaskiya. Shi ma hakan na birge shi ainun, shi da kansa yake karfafa min gwiwa. Kuma dadin-dadawa ma a lokacin ni ce amarya to, yana ji da ni sosai. 

Wacce shawara za ki bai wa matasan mata da ke sha’awar aikin banki? 

To, shawarwarin da zan ba su dai lallai ne su sa a ransu suna son aiki, kuma su nuna kwazonsu a kan aikin da ke gabansu, don karatun da suka yi ya yi musu amfani, ba tare da an samu wani kuskure ko rashin gaskiya a aikin su ba. Sannan su tsaya su yi aikin da ke gabansu ba tare da sun sa wasa ko sharholiya da abokan aiki ba. Saboda shi aikin banki aiki ne mai kima da mutunci, ba a son mutum marar kamun kai da natsuwa. 

Yaya ki ke ji a ranki yadda yanzu aikin banki ya zama? 

Gaskiyar magana aikin banki yanzu ya yi sauki sosai, ganin yadda komai ya koma kwamfiyuta. An samu saukin tafiyar da aikin, kuma an samu saukin aikata rashin gaskiya. Yana da kyau a ce ana horar da yara masu tasowa a aikin banki, muhimmancin tsare gaskiya da rikon amana, domin a magane cin amana da wasu abubuwa na kurakurai da ake tafkawa yanzu. Amfani da kwamfiyuta da yanzu ake yi ya bai wa wasu gurbatattun ma’aikata damar yin abubuwan da ba daidai ba. Don haka ya kamata Babban Bankin Najeriya su vullo da wasu dabaru na toshe duk wata baraka da wasu gurbatattun ma’aikata za su amfani da ita wajen cutar jama’a. 

Yaya ki ke ji a ranki da badakalar da aka bankado tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele yana da hannu wajen ayyukan rashin gaskiya da ta’asa da ake ganin ya shirya da wasu ma’aikatansa ciki har da mata? 

Gaskiya yanzu zamani ya lalace, abin takaici ne yadda za a ce wai ga wata mace an samu hannunta dumu dumu cikin wata almundaha. Ba dabi’ar mace ba ce a same ta cikin ayyukan rashin gaskiya. Ba a san mace da halin vera ba, sam! An fi sanin mu wajen neman na kanmu, da neman rufawa kanmu asiri da iyalinmu, da ma al’umma bakidaya. Abin da Emefiele ya yi ya nuna rashin gaskiya ne da rashin imani da ma rashin tausayi yadda ya rika kwasar dukiyar kasa yana arzuta kansa. Saboda munin abin da ya yi ma ko tausayinsa ba a ji. 

Tun tasowarki wanne buri ki ka taso da shi a rayuwarki? 

To, a gaskiya na taso da sha’awar in ga na zama wata mace da ta cimma nasarori a rayuwarta. Lokacin ina makarantar sakandire a Queen Elizabeth School, na ga yadda wasu mata musamman Yarabaw yadda suke da himmar samar wa kansu cigaba, daukaka, fice a fannoni daban. Daga cikin matan da suke ban sha’awa, kuma nake kallo a matsayin madubin rayuwata, akwai irin su Maryam Abacha, Hajiya Binta Ƴar’aduwa, da mai shari’a Fati Abdulsalami Abubakar, dukkansu sun yi makarantar da na yi ta Queen’s School, kuma sun taimaka wa cigaban rayuwa. Ni ma da haka na taso a zuciyata, don in zama babbar ma’aikaciya kuma mai taimakawa na kasa da ni. Shi ya sa ban taba sha’awar zaman gida ba. 

Me ki ke so ƴammata masu tasowa su yi koyi da shi daga rayuwarki? 

To, ni da mace ce da bani da, son rigima, don rigima ba ta da amfani. Sannan su zama masu wadatar zuci, kar su zama masu kwadayin tara abin duniya. Har-wa-yau kuma ina son matan yanzu su san muhimmancin rike gaskiya. Idan mace ta rike gaskiya, kowa zai yarda da ita kuma za a mutunta ta. Ba na son a tsare ni a zarge ni da wani abu na rashin gaskiya. Don mun taso tun muna yara an tarbiyyar da mu a kan tsare gaskiya da kiyaye doka. Mahaifinmu ma’aikacin gwamnati ne mai kokarin tsare gaskiya a ayyukansa. Ƴammatan yanzu idan sun rike gaskiya za su ga komai nasu na tafiya daidai. 

Yaya ki ke kallon kalubalen malamai wajen koyarwa, duba da yadda ake kokawa da tabarbarewar tarbiyya a tsakanin dalibai? 

Al’amarin tavarvarewar tarbiyya daga gida yake samo asali, idan iyaye suka yi sako-sako da tarbiyyar ƴaƴansu shi ne ake samun lalacewa yara, har ma kuma su zo makaranta su hadu da wasu kangararrun yaran. Tun yaro na karami ya kamata iyaye su nuna masa abin da ya yi ba daidai ba ne ko kuma ya yi daidai. Rashin tsawatarwa yara tun a gida shi yake sa idan ya je makaranta ya cudanya da wasu yaran sai ka ga an samu matsala. Duk kokarin malami wajen tsawatarwa yara, sai iyaye sun dafa musu. Tarbiyya ba ta yiwuwa ta bangare guda. Nauyi ne da ke kan iyaye, malamai, da ma al’umma baki daya. 

Mu je ga batun matsayin da ki ke riqe da shi na shugabar Jam’iyyar Matan Arewa a nan Jihar Filato. 

To, a gaskiya matsayi ne wanda ba nema na yi ba, an zo ne an same ni da shi, mai yiwuwa bisa lura da yadda nake tafiyar da harkokin rayuwata ne, da aikin da nake yi. Don an zo har gida ne aka min tayin shiga cikin tafiyar yunkurin farfado da tafiyar kungiyar, bayan an gamsar da ni na yi shawara a gida, kafin na amince na karfi jagoranci tafiyar. Ni ce nake wakiltar matan Filato a karkashin wannan kungiya. 

Wadanne ayyuka ku ke gudanarwa a nan Jihar Filato? 

To, dama manufofin kungiyar sun hada ne da koyawa mata hanyoyin da za su iya rike kansu, sannin hakkokinsu, da yaki da shaye-shaye a tsakanin matasa maza da mata, da dora su a kan turba ta tarbiyya. Sannan akwai batun rike yara marayu ko wadanda ake zubar su a titi, saboda ba a same su ta hanyar aure ba, muna karbarsu mu kula da rainonsu da dan abin da muke da shi. 

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki? 

Zaman duniya iyawa ne! 

Na gode.

Ma sha Allah. Ni ce da godiya