Rubutu makami ne mai dafi da za a iya sokar ahalin marubuci da shi – Faisal Hunkuyi

“Marubuci madubi ne mai ɗauke da majigin nazarto gaba da baya”

Daga AISHA ASAS

Shafin Adabi na wannan mako ya sakulo wa masu karatunmu daya daga cikin jajirtattun matasan da ke yi wa adabi hidima. Kokarin sa da nacewa wurin ganin ya kwankwade duk wani kalubale da ya yi tuntube da shi a hanyar sa ta zama marubuci abin a yaba masa ne.

Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Faisal Haruna Hunkuyi;

MANHAJA: Za mu so ka fara da bayyana kanka ga masu karatunmu.

FAISAL HUNKUYI: Sunana Faisal Haruna Hunkuyi. An haife ni a cikin garin Hunkuyi da ke Karamar Hukumar Kudan a Jihar Kaduna. Na yi primary da secondary school di na duk a garin Hunkuyi kafin in wuce Jami’ar Jihar Kaduna (Kaduna State University) inda anan na samu shaidar kammala digiri na farko a bangaren noma da kiwo tare da tsare-tsaren shige da ficen kayan noma (General Agriculture). Ta bangaren Islamiyya nan ma an sha fafutuka kwarai har kawo yanzu kuma akan doron fafutukar ake.

Kasancewar rubutu na da rassa da yawa. Za mu so sanin bangaren da ka fi kwarewa.

Mafiyawancin rubutuna na fi maida hankalina akan yadda zamantakewa a gidajen ma’aurata ke yin tsami; na kan shiga in zakulo wani abu da ya kan zama silar ruruwar wutar da ke yaduwa a cikin gidaje domin in nusar da vangaren da abin ya shafa. Duk da yawancin masu karanta rubutuna suna yi min tambayar ‘ni likita ne?’ Ba komai ya sa suke yi min wannan tambayar ba kuwa illah ganin duk takardar da zan dora alqamina a kanta to na kan yi kokarin shigo da wata cuta da ta addabi al’umma in warwareta sannan in kawo mafita.

Ka yi zancen makaranta littafanka na yawan tambayar ko kai likita ne. Shin ta yaya ka ke iya samar da gamsashen bayyani kan harkar lafiya alhali kai din ba likita ba ne?

Ina samar da gamsasshen bayani ta hanyar tuntuvar kwararrun likitoci kasancewar ina da kyakkyawar fahimta tsakanina da su, idan na dauki wani bangaren har asibiti ina zuwa in gani da idunana sannan in yi tambaya.

Ko za ka kai mu ga lokacin da ka fara dora alqalami da zumar rubuta labari?

Na fara dora alkalami a bisa takarda tun 2008, ina JSS 2 a lokacin. Sai dai rashin karfin gwiwa da ban samu ba tare da yadda abokaina suke yi min dariya ya sa na watsar da harkar. Duk da a lokacin idan na rubuta kuma su kan zo su dauka su karanta har tambayoyi su biyo baya. Ba zan manta ba akwai mahaifiyar wani abokina idan ta ji suna yi min dariya ta kan kira ni har ta karbi aikin da na yi ta karanta sannan ta fara jinjina min, ba qaramin dadi na ke ji ba a lokacin.

Wadane kalubale ka fuskanta kafin burin naka na zama marubuci ya tabbata?

Kalubale fa kam an hadu da su birjik, sai dai wani ya fi wani kawai.

Na farko; Na fara rubutu ban san kowa ba haka babu wanda ya sanni duk da lokacin da na fara Facebook 2012 na yi matukar kokari wajen bibiyar marubutan da ludayinsu ke kan dawo a wancan lokacin. Sai dai kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Yawancin marubutan da na bibiya da zarar na je da kokon bara ta basa sake yi min magana wannan ya sa harkar ta kara fita a raina. Akwai wanda a satin da ya wuce ma na buxe ‘messenger’ ina bincike na ci karo da sadon da na fara tura masa wallahi har yanzu bai bude ba balle ya bani amsa.

Na biyu; A lokacin da na ke ganin burina na zama marubuci ya kusa cika, a lokacin kuma ba ni da zabin da ya wuce in yi hakuri kasancewar na koma jami’a sannan ina ganin hada taura biyu a bakina ba zai ba ni sakamako mai kyau ba.

Na uku; A yanzu kalubalen bai wuce yanayin yadda ake shigar da labaran ba bayan an rubutasu tun daga ‘Online’ din har ‘Publishing’ din kowanne cike yake da na shi salon kalubalen.

Idan na fahimce ka babu marubucin da ya taba ba ka taimako a lokacin da ka ke fafutukar zama marubuci?

A wancan lokacin gaskiya babu, sai a shekarun da ba su uku zuwa hudu ba da Allah ya Tarawa garina nono na yi gam-da-katar da wasu zakakuran marubuta guda biyu a lokuta mabambanta. Kowanne a cikinsu na bayyana masa burina kuma suka amsheni hannu bibbiyu tare da karfafa min gwiwa don daya a ciki gar da alkawarin zai shige min gaba wajen wallafa labarina na farko.

Dayan kuwa ya yi matukar kokari wajen ajiye duk wasu ayyukansa ya bibiyi rubutuna inda ake bukatar gyara ya gyara inda kuma ake bukatar shawara ya bani. Kuma har kawo yanzu ko tari zan yi indai a harkara adabi wadannan mutum biyun sai sun tuntubi dalili.

Shin kana buga labaranka zuwa littafi ko kuwa a iya onlayin ka tsaya?

Ina buga su a takarda sannan ina dillancinsu onlayn.

Zuwa yanzu ka rubuta littafai nawa?

Dogayen labarai za su kai guda biyar sai dai guda daya ne na buga shi a takarda sannan yanzu haka ina shirin fitar da wani a wannan lokacin In sha Allah. Akwai; ‘Makauniyar Zuciya’, ‘Kisan Boko’, ‘Bahaguwar Rayuwa’, ‘Bokiti Mai Yoyo’, ‘Duniyar Gizo’, ‘Son Zuciya’.

Ko za ka sanar da mu abinda biyu daga cikinsu ya kunsa?

Akwai ‘Makauniyar Zuciya’ wanda labarin wasu masoya ne da su ka jima suna dakon soyayyar junansu sai da aka zo gaf da cikar burinsu gwajin jini (Genotype) ya kawo masu cikas. Tun daga asibitin suka lalata sakamakon da aka ba su, abokinsa da ya yi masu rakiya suka bata sakamakon tunatar da shi illar da ke tattare da abinda su ke shirin yi. Sun boyewa kowa har aka daura musu aure. Rayuwar aurensu gwanin ban sha’awa har zuwa lokacin haihuwa ta fara yi musu sallama kuma suka fara da abinda ake hango musu a jere sun haifi yara biyu masu dauke da amosanin jini.

Daya ya mutu ya bar daya, tsananin talauci da wahalar da suke ciki ya sa mijin ya gudu ya bar matar da yarinyar a gadon asibiti, hakan ya harzuka iyayenta har suka raba ta da tilon yarinyar da ke kwance tsakanin mutuwa da rayuwa. A karshe dai sun dawo sun hadu bayan wasu shekaru.

‘Kisan Boko’; Labarin wata ce da ba ta nemi komai ta rasa a duniya ba sai abu daya da ya yi mata bayan ta same shi kuma ta banzatar da shi shi ne; Aure. Ta dade tana yi wa kanta huduba da “Ba a haxa gudu da susan katara” ta biyewa kyawun jiki da cincirindon samarin da ke faman fareti a kofar gidansu ko yaushe.

Ta ba karatun boko muhimmanci fiye da komai har zuwa lokacin da ta gama digirin farko ta fara na biyu. Ta fara kuka da idanuwanta a lokacin da ta nemi samarin nan ta rasa ga tsufa ya doka sallama.

Ko rashin samun goyon bayan manyan marubuta ga marubuta masu tasowa zai iya kawo tawaya a cigaban harkar rubutu?

Gaskiya sosai yana kawowa ne ma ba wai zai kawo ba. Domin ko ranar Alhamis na yi magana da wata da ke da burin fara rubutu sai dai abinda ke sagar mata da gwiwa ta bibiyi manyan maruta da dama amma babu wanda ya saurareta. Sannan, akwai wani ‘conference call’ da aka hada a wani guruf a manhajar whatsapp an samu akalla mutane biyar da suka shigar da korafi makamancin wannan.

Kin ga kenan rashin samun goyon bayan manyan da suka jima a fagen ba karamin tawaya zai kawo a fuskar rubutu ba.

Wa ake cewa marubuci?

Marubuci wani mutum ne wanda yake nazari da binciken rayuwa da halayyar jama’ar da yake zaune tare da su, sannan kuma ya dabbaka rubutunsa domin fayyace ainihin daidaitacciyar hanya wacce kowa ya kamata ya bi. Marubuci yana da wata baiwa ta musamman da Allah ya ba shi, wacce da ita ne yake iya tsara maganganun da za su nusar da makarancin rubutunsa illar wani abu da ya yi masa karan tsaye a zuciya. Marubuci yakan yi tunani irin na mutane da dama, walau bai taba rayuwa a cikin su ba, ko kuma akasin haka.

Marubuci wani madubi ne mai dauke da majigin nazarto wani abu da zai faru ko kuma ya taba faruwa a wani karni na can baya sannan ya kan iya hasashen abinda zai faru a gaba ma.

Idan da za a ba ka damar kawo sauyi a matsaloli da ke ci wa marubuta tuwo a kwarya, wacce matsala ce ka ke ganin za ka kawo hanyar magance ta?

Akwai matsalolin da ke ci wa marubuta tuwo a kwarya birjik amma matsalar da na ke hangenta a babbar matsala duk da wasu za su kalle ta a ba ta kai ta kawo ba ba ta wuce; ‘Yan ‘downloading’ ba, idan na ce ‘yan ‘downloading’ ina nufin ma su zuwa su dauki littafi ba tare da izinin marubuci ko marubuciyar ba su karanta shi da muryoyinsu domin gyara tukunyar gidansu kinga anan an yi kura da shan bugu gardi da kwasar kudi.

Idan ki ka je YouTube za ki samu littattafan marubuta sosai wadanda ba su da masaniyar yadda aka fara karantasu har aka dora a YouTube din ma. Wannan ba qaramin koma baya ba ne ga marubuta duk da salo ne na ci gaban zamani. Kuma samun ‘audio’ din da ake yi ya taka muhimmiyar rawa wajen dakile karatu a takarda ko a onlayin din ma.

A mahangata hukumomin da abin ya shafa ya kamata su yi tsayin daka wajen dakile yawaitar wannan matsalar kamar yadda ‘yan fim su ka dinga fafutuka a lokacin da su ka fuskanci makamancin wannan matsala ta satar fasaha.

Na biyu; Yadda kasuwar littafi ke tafiya a onlayin din shi ma akwai gyara sosai domin ni har na gwammace ma in samu masu siyen labarina a takarda in buga in ba su su bani sulallana akan in kai shi onlayin. Dalilina kuwa shi ne; marubuci ko marubuciya za su bata dare wajen tsara rubutunsu a karshe a onlayin din idan ba za su bada na bulus ba bai wuce mutum uku zuwa biyar ne za su iya cire kudi su siya, wadannan mutane biyar din idan su ka siya to ki kaddara tamkar kin sakarwa duniya labarin ne. Akwai marubuciyar da ke bani labarin har ‘group’ ake budewa da ake tura irin wadannan labaran da ake siyarwa.

A wannan gabar in da zan samu dama zan kirkiri wata manhaja ce da za a riqa saka littafi a ciki tana ba da lambobin sirri mabambanta (password) ta yadda idan Bala ya siya to lambobin da zai sa ya bude littafin ya bambanta da na Shehu. Sannan a cikin manhajar zan saka abin da zai hana littafin budewa a ko wacce waya face ainihin wayar da aka fara bude shi da ita. Faruwar hakan zai dakile yawaitar tura labarin da aka siya ba tare da izini marubuciyar ko marubucin ba.

A wane yanayi ka fi jin dadin yin rubutu?


Ina jin dadin rubutu a lokacin da na ke halin kadaici, babu dare ko rana ko yaushe matuqar zan kasance ni kadai a wurin da babu hayaniya kuma bani da wani aiki, to tabbas; zan dora alkalamina akan takarda.

Ta ya ka ke samun jigon rubutu idan za ka yu?

Akwai hanyoyin samun jigo da yawa, domin idan ki ka kalli rayuwarmu ta yau da kullum zagaye mu ke da mabambantan jigon da suke bukatar a taba su. Na fi daukar jigo a lokacin da na ci karo da faruwar wani al’amari da ya daure min kai. Na kan tsaya in yi duba na tsanaki sannan in lalubo manufar faruwar al’amarin daga nan zan duba ta yadda idan saka zaren labarina zai yi hannun riga da wannan abu da ya faru kuma na gani domin vatar da sawuna gudun tuhumar na kwafi rayuwar wasu. Ma fi yawan labarina gaskiya abu ne wanda ya faru a zahiri kuma na gani da idanuna.

Menene burinka a harkar rubutu?

Rai cike yake da buri, babu wani mai rai da zai bar duniya ba tare da buri ba.
Burina a harkar rubutu bai wuce Allah ya bani ikon in samar da wani littafi wanda za a dinga tunawa da ni ta dalilinsa ko bayan mutuwata kuma ya zama wannan littafin har a tsangayar ilimi za a iya nazartarsa.

Zuwa yanzu ya za ka iya bayyana nasarar da ka samu a harkar rubutu?

Nasarori kam Alhamdulillah! Domin, ko wannan hirar ma ai babbar nasara ce. Sannan na shiga gasanni mabambanta na fafata da manyan marubutan da idan a zahiri aka sanar da ni zan iya fafatawa da su ba zan yarda ba, kuma Alhamdulillah duk gasar da zan shiga ko da ban fito a sahun gwaraza ba, na kan fito a cikin ‘top’ 10 din da aka zaba. Gare ni wannan babbar nasara ce sosai.

Sannan, silar rubutu na hadu da mabambantan mutane wadanda zumunci mai karfi ya kullu a tsakanina da su har ta kai sukan dauki damuwata ta zama ta su. Babbar nasara ce wannan a rayuwa. Bugu da kari matata kafin mu yi aure bayan ta samu kwafin littafin da na wallafa ta dinga yawo da shi tsakanin kawayenta tana daga kafa da bada labarin marubuci za ta aura, (dariya).

Har aka samu wata da ta fara neman kulla alaka da ni domin ta nuna nata kwazon a harkar rubutu. To kin san kishin mata, tuni ta bi ta toshe duk hanyar da wannan kawar tata za ta same ni. Nasara babba.

Wacce shawara za ka ba wa marubuta masu tasowa?

Shawarata ga marubuta masu tasowa bai wuce; su yi hakuri su jajirce sannan duk abinda alkalaminsu zai rubuta su tabbatar da ingancinsa domin shi kan shi rubutu wani makami ne mai dafi da za a iya amfani da shi a soki ahalin marubuci. Sannan a tsananta bincike akan dukkan jigon da aka dauka.

Ko kana da kiran da za ka yi ga manyan marubuta?

Kira na ga marubuta ne gabadaya yakamata su sani cewa; Idan kaine yau ba fa kaine gobe ba. Kuma a duk inda za a ambaci sunan wane ko wance ba karamin abun alfahari ne a ji wasu da suka fito daga wani bangare sun zo suna dukan kirji suna kirarin yadda ka/ki ka taimaka musu wajen cikar burinsu ba. Sannan, magana mai dadi ita ma sadaka ce. Ko ba zaka taima ki mutum ba, ka/ki ba shi wasu mintoci ko da gaisuwarsa ne ka/ki amsa.

Marubuta ‘yan’uwan juna ne ni ma shaida ne. Mu kara zage damtse wajen karfafa zumuncinmu sannan duk inda aka samu mai burin dora alqalaminsa akan takarda a taimake sa/ta da ‘yan shawarwari.

Mun gode.

Ni ma na gode kwarai.