Matsin Rayuwa: Ku ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu, sauƙi na tafe – kiran Idris ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kara hakuri da gwamnatin Shugaba Tinubu bisa sauye-sauyen da take yi don cigaban kasa.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya yi wannan kira, inda ya ce watannin da Tinubu ya yi a ofis ba su taka kara sun karya ba balle a rika kukan rashin gani a kasa.

Tun bayan da ya kama mulkin kasa a watan Mayun da ya gabata, Tinubu ya dauki wasu matakai ciki har da cire tallafin mai lamarin da ya jefa kasa cikin halin tsadar rayuwa.

Sai dai Idris ya ce ya yi amannar akwai yiwuwar a fuskanci hakan, tare da cewa za a ci ribar sauye-sauyen nan gaba.

Ministan ya yi wannan bayani ne a wani shiri da aka yi da shi a tashar Channels Television a ranar Alhamis.

“Ina so ku tuna cewa wata bakwai kacal Shugaban Kasa ya yi a ofis. Ba zan ba da uziri ba cewa wata bakwai lokaci ne kankani.

“Amma a tsare-tsaren dogon zango, zai dauki tsawon lokaci kafin a fara cin moriya. Dole a rika cin karo da matsi yayin da tafiya ta yi tafiya. Sai dai manufar Shugaban Ƙasar a bayyane take, so yake Nijeriya ta bukasa yadda ya kamata.”

Ya kara sa cewa Shugaban Kasa na aiki ba dare, ba rana don cimma wannan manufa. Yana mai cewa, gwamnati na sane da halin matsin da ‘yan kasa ke fuskanta, tare da bai wa al’ummar kasa tabbacin gwamnatin na yin bakin kokarinta domin samar da walwala ga ‘yan kasa.