Tsaro: Tsarin da ake bi ba shi da tasiri – Kakakin Majalisar Wakilai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajuddeen ya bayyana a ranar Talata cewa Majalisar Tarayya za ta yi taro na musamman dangane da gagarimar matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya baki daya.

Ya bayyana haka yayin da aka koma zaman majalisa, inda ya ke cewa matsalar tsaro a kasar nan ta yi muni kuma ta kazanta matukar gaske.

“Ina bada shawarar gudanar da Taron Majalisar Tarayya kan Matsalar Tsaro. Taron zai kasance ya zama wurin da za a bijiro da shawarwari daga bakin masu ruwa da tsaki a bangarori da dama, kamar jami’an tsaro, sarakunan gargajiya, malaman addini, masana daga jami’o’i da cibiyoyin ilmi, kungiyoyi da sauransu.”

Abbas ya ce hakan zai “shimfida mikakkar hanyar da za a bi domin a kawo karshen matsalar tsaro.

“Lokaci ya yi da za mu taru mu kawar da duk wata miskilar da ke kawo cikas wajen dakile matsalar tsaro. Idan mun yi haka, za mu wanzar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki a kasar nan,” inji shi.

Abbas ya ce maganar gaskiya da tsarin da a yanzu ake kai wanda ake bi don ganin an daqile matsalar tsaro, ba shi da wani tasiri.
Daga nan sai ya yi kira ga Shugaba Tinubu ya tashi tsaye ya sauya tsarin kwata-kwata.

Ya shawarci Tinubu ya kara matsa wa manyan hafsoshin tsaron kasa lamba, kuka idan ta kama ya dauki wani tsatsauran mataki a kan su, to ya gaggauta dauka.

“Idan ma ta kama a yi wani gagarimin garambawul a cikin manyan tsaron kasar nan, to a hakan, domin lamarin ya na neman gagara fa.”

A ranar Litinin ce dai wannan jarida ta buga labarin cewa wasu kungiyoyi 48 sun ce lokacin kafa dokar-ta-baci kan matsalar tsaro ya yi, bayan kashe mutum akalla 2,343 a watannin mulkin Tinubu.

Wasu kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam da kare dimokradiyya sun yi kakkausan kira ga Shugaba Bola da ya gaggauta kafa dokar-ta-baci kan matsalar tsaro.

Kungiyoyin su 48 sun bayyana wannan matsaya ta su a wani taron manema labarai na duniya da suka kira a Abuja, ranar Litinin din nan.

Babban Daraktan CISLAC, Auwal Rafsanjani, wanda ya yi jawabi a madadin sauran kungiyoyin, ya ce su na cikin nuna matukar damuwar su dangane da yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a kasar nan.

Daga nan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye haikan ta magance wannan matsala.

“Gangamin kungiyoyi a karkashin ‘Civil Society Joint Action Group, Community of Practice Against Mass Atrocities, and Nigeria Mourns, sun damu kwarai dangane da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a fadin kasar nan, har da Abuja, Babban Birnin Tarayya, FCT da kewaye.

“Dangane da haka ne mu ke yin kira ga Gwamnatin Nijeriya ta yi gaggawar tashi tsaye ta kawo karshen wannan yawan garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda, kuma a binciki yawan mutanen da suka vace sanadiyyar hare-haren da ake kai masu,” inji Rafssanjani.

Ya ce matsalar tsaro ta ci gaba tun daga gwamnatocin baya guda uku, ciki kuwa har da ta tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda shi tsohon Janar din soja ne, wanda ‘yan Nijeriya su ka damka masa amanar kare lafiya da rayukan su, amma hakan bai samu ba a lokacin mulkin sa.

Rafsanjani ya ce a zangon mulkin Buhari na biyu daga 2019 zuwa 2023, an kashe mutum akalla 24,316 a Nijeriya, sannan kuma an yi garkuwa da mutum 15,597 duk a lokacin.

Ya kara da cewa a iyakar watannin da Tinubu ya yi kan mulki daga Mayu 29, 2023 zuwa Janairu 2024 na mulkin Tinubu, an kashe mutum 2,423, sannan an yi garkuwa da mutum 1,872.