Bayan gasar AFCON Peseiro zai san makomarsa – Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kwallon Kafar Nijeriya, ta bayyana cewa babu wata yarjejeniya da ke tsakaninta da kocin tawagar Nijeriya a gasar kofin Afirka ta AFCON da ke gudana a kasar Ivory Coast, Peseiro Wary bayan kammala gasar.

Shugaban hukumar Ibrahim Musa Gusau ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.

Ya kara da cewa, “abin farin ciki yanzu shi ne duk wasu basuka da yake bi, mun samu daga Gwamnatin Tarayya za a biya shi.”

Sai dai ya ce, za su iya daukar koci daga kowace irin kasa ta duniya ba lallai sai dan Nijeriya ba.

“Abin da ake so shi ne a samu wanda zai saita ‘yan wasa, kwararre wanda zai samar da sakamako mai kyau”.