Filato: An fara raba kayan aikin zaɓe babu tambarin PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara rabon muhimman kayan zabe a kananan hukumomi shida na jihar Filato gabanin zaben da za a sake gudanarwa ranar Asabar.

An yi rabon kayayyakin zaben ne a harabar Babban Bankin Nijeriya da ke Jos, babban birnin jihar.

An gudanar da rabon kayayyakin ne a gaban wakilan jam’iyyun siyasa, masu sa ido, ‘yan jarida da jami’an tsaro.

Sai dai da aka fara rabon kayayyakin, an gano cewa babu tambarin Jam’iyyar PDP a takardar jefa kuri’a yayin da wasu da suka hada da APC, PRP, da LP duk suna a kan katin zaben.

Lamarin ya haifar da cece-kuce a yankin yayin da aka ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP da suka hallara don shaida yadda aka raba kayan zaben suna nuna rashin amincewarsu da rashin shigar da jam’iyyarsu tare da zargin INEC da yin adawa da hukuncin kotun daukaka kara da ta ce dukkan jam’iyyun da ke takara za su shiga zaven.

A ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan jam’iyyar PDP da magoya bayansu a jihar Filato suka gudanar da zanga-zanga a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta da ke Jos kan zargin fitar da jam’iyyar a zaben da za a yi a ranar 3 ga Fabrairu, 2023, amma jami’n hukumar zave ya ba su tabbacin cewa za a kula da lamarin.

Masu zanga-zangar sun bukaci shaidar shigar jam’iyyar PDP a zaben Sanatan Filato ta Arewa da kuma mazabar Bassa/Jos ta Arewa inda za a sake zaben ranar Asabar.

Kafin zanga-zangar dai an yi ta raɗe-raɗin cewa jam’iyyar PDP da ‘yan takararta ba za su sake shiga zaben ba bayan hukuncin kotun ɗaukaka kara da ta soke zaɓen da aka gudanar a mazaɓu biyu da ‘yan takarar jam’iyyar suka yi nasara a baya Sanata Simon Mwadkwon na Filato. Arewa da Musa Agah, mai wakiltar Jos North/Bassa.