Idan za ki shiga fim ki nemi daraktan da ba jikinki zai nema ba – Fatima Umar

“Muddin ka shiga fim da sa bakin iyaye za kai nasara”

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Fatima Umar sabuwar jaruma da ta shigo Kannywood da kafar dama, inda a cikin kasa da wata uku ta yi finafinai har guda 10. A tattaunawar ta da wakilinmu a Kano, za ku ji tarihinta da kuma irin nasarorin da ta samu ya zuwa yanzu.

MANHAJA: Da wa muke tare?

FATIMA UMAR: Sunana Fatima Umar. Ni ƴan asalin Kasar Nijar ce, amma a yanzu iyayena suna zaune a Kasar Binin, Ni kuma ina zaune a Jihar Katsina . Na yi primary da secondry har zuwa kwaleji duk a Kasar Birnin, amma da Faransanci duk na yi karatun.

Me ya kawo ki Nijeriya?

Aure ne ya kawo ni Nijeriya, shekara hudu da ta gabata, a Katsina, amma yanzu auren ya mutu shi ne na ci gaba da zama Nijeriya.

Ya a ka yi kika shiga masana’antar fim ta Kannywood?

A gaskiya ban fi wata biyu ba da shigowa Kannywood.

Me ya baki sha’awa kika shiga masana’antar Kannywood?

Harkar fim tana ba ni sha’awa tun ina karama, muna kallo a talabijin yana ba ni sha’awa yana burge ni.

Ba ki hadu da ƴan kan ta waye ba?

Gaskiya ban fuskanta ba, domin ko shi wancan fim din da na fara yi ina zaune aka kira ni a ka ce za a yi fim din na ‘Sauyi’. Amma dai muna cikin Kannywood din ba mu sani ba, lokaci ne zai nuna.

Kin ce iyayenki suna Kasar Binin. Ko sun san kin shiga Kannywood?

Sun sani da izininsu na shiga.

Da wane fim kika fara?

Da wani fim ne mai suna ‘Sauyi’, da shi na fara.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa kika yi?

Gaskiya ya zuwa yanzu ba su fi guda 10 ba.

Kenan kin shigo da kafar dama?

(Dariya) gaskiya na gode wa Allah.

Bangaren wakoki fa?

A vangaren waka, bidiyo ne na waka ake saka ni a ciki, kuma daga lokacin da na fara, na yi wakoki kamar guda biyar.

Wasu mutanen har zuwa yanzu ba sa fahimtar ƴan fim inda suke cewa suna latata tarbiyya. Me za ki ce?

Gaskiya duk wanda ya zagi ƴan fim sai dai mu ce Allah ya saka masa, domin idan ka dauki fim a sana’a to ka dauke shi a haka, wai a ce sai diya ta lalace sannan za a sanya ta cikin fim to ba gaskiya ba ne, ita wannan harkar tamu ta fim muddin ka shigo da sa bakin iyaye to za kai nasara. Shi fim fa aiki ne mai wahala wanda in dai ba kana ciki ba ba za ka gane haka ba, amma surutu ko cece-kuce da wasu suke yi a kanmu mu to daukar alhakinmu suke yi.

A lokacin da aka fara dora ma ki kyamara ba ki rude ba?

Farkon dora min kyamara wata wakar siyasa ce da muka yi ta ‘Gwamnan Katsina Dikko Radda’, amma gaskiya na ji wani iri, don hatta maganar da na yi a gurin muryata rawa ta dinga yi, da ya ke shi ne na farko amma yanzu da ikon Allah gogewa a ke yi.

A cikin finafinan da kika yi wane fim ne ya ba ki wahala a lokacin da ake daukar sa?

A cikin fim din ‘Hallacci’ akwai wani wuri inda na yi wa Nafisa tsawa a falo, to da yake ni ban iya harkar fada ba, sai sai da a kai ta maimaitawa wurin ya bani wahala gaskiya.

Menene kiran ki ga sabbin jarumai masu shigowa Kannywood?

Shawara ta gare su shi ne, idan za su shiga fim su yi kokari su samu darakta ko ‘producer’ kai tsayayye, wanda ba jikinki zai nema ba ko wani abu daban ba, wanda zai yi maki abinda kike so. Kuma ina ba su shawara a duk lokacin da za su shiga fim ko wani abu na rayuwa to su nemi addu’ar iyaye, ba cece-kucen dangi ba, domin iyaye su ne gaba da kowa.

Wane kira da ki yi ga ‘Producers’ da daraktoci?

Kira na shi ne su rinka jarraba sabbin jarumai, domin wani manyan wani lokacin ba sa samun damar zuwa, watakila saboda aiki ya yi masu yawa, gwara a irinka gwada sabbi su ma.

Menene burinki a Kannywood?

Burina shi ne na samu kudin da zan taimaka wa gidan marayu da gidan gajiyayyu da masu karamin karfi, don ni ban damu da sai na yi fice ba.

Mun gode.

Ni ma na gode kwarai.