MOPPAN ta naɗa Habibu Barde Shugaban Riƙo na Ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta nada Mataimakin Shugaba na Shuyyar Arewa ta Tsaki, Malam Habibu Barde, a matsayin shugaban riko na kasa na kungiya.

Sanarwar nadin na kunshe ne cikin sanarwar manema labaran da Kwamitin Amintattu na kungiyar ya fitar a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugabansa, Makama Sani Mu’azu.

Sanarwar ta kuma nuna cewa nadin Barde a matsayin Shugaban riko na kungiyar ya fara aiki ne nan take.

A cewar danarwar, “Nadin ya biyo bayan ajiye mukaminsa da Dr. Ahmad Sarari ya yi ne a matsayin Shugaban Kungiyar.”

Keamitin ya nuna godiyarsa ga Dr Ahmad Sarari bisa dawainiyar da ya yi da kungiyar wajen ciyar da ita gaba a tsakanin shekarun da ya shafe rike da ita.

MOPPAN na daga cikin fitattun kungiyar masu shirya finafinai a Nijeriya mai mamabobi da dama da kuma rassa a fadin kasa.