EFCC ta bankaɗo ƙungiyar addini tana samo kuɗin ɗaukar nauyin ta’addanci

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta bankado yadda wata kungiyar addini a Nijeriya ke tafka almudahana don daukar nauyin ta’addanci.

Kazalika ya bayyana yadda suka sake gano wata kungiyar addini da ke ba da kariya ga wani mai karkatar da kudade bayan gano wasu kudade a asusun kungiyar da ake zargin na sata ne.

Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a ranar Larabar a cibiyar Musa Yar’Adua da ke Abuja, yayin wata tattaunawa ta yini daya kan “Matasa, Addini da Yaki da Rashawa.”

A cewar Olukoyede, EFCC ta yi nasarar bankado kungiyoyi da cibiyoyinaddini da laifin karkatar da kudade.

“An samu wata kungiyar addini da ke karkatar da kudade don daukar nauyin ‘yan ta’adda,” in ji Olukoyede.

Tun farko, ya bayyana cewa, “Mun yi kokarin gano wasu kudade da aka karkatar da su zuwa asusun kungiyar addini, amma da muka je muka sami cibiyar don gudanar da bincike sai muka samu umarni a kan mu dakatar da binciken.

Ya ci gaba da cewa, hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa game da binciken domin kuwa za ta daukaka kara kan umarnin domin samun damar ci gaba da binciken nata.

Ya ce tun bayan da ya zama shugabanta kimanin watanni uku da suka gabata, EFCC ta samu nasarar gurfanar da masu laifi 747.