Matsayin wasan kwaikwayo (fim) a yau

Daga MUHAMMAD UBALE ƘIRU

Kafin na shiga cikin wannan maudu’i, ina so mai karatu ya fadada fahimtarsa a kan wannan batu, ya kuma yi hakurin karanta wannan rubutu har zuwa karshe kafin ya yi raddi ko fassara ga wannan maudu’i. Sannan yana da kyau mai karatu ya sani cewa, wannan ra’ayi ne da kuma fahimta irin tawa, kuma hakki ne na ilimi ka bai wa kowa damar tsayawa a kan wani ra’ayi ko furta fahimta.

Da farko, makasudin wannan rubutu shi ne don karin haske ko fadada bayani a kan wani batu da Shaikh Malam Ibrahim Khalil ya fara tattaunawa a hira da aka yi da shi a kan yadda ya yi ta kokari wajen ganin an samar da ‘Masana’antar Fim’ a Kano. 

To, mene ne Masana’antar Fim? Masana’antar Fim wata masana’ata ce da ake kirkire ta don zama wani sanannen waje na musamman da ake kirkirar fina-finai, sarrafa su, da kuma shirya su. Guri ne wanda yake dauke da dakunan shirye-shirye na musamman, wanda ba dole sai shirin fim ba, kai har abin da ake kira da dakunan gabatarwa ta yanar gizio wadda za su ba ka dama ka shirya abu tamkar kana wata nahiyar ta duniya.

Kuma ita Masana’antar Fim a ko’ina a duniya ba don shirin fim kadai ake kirkirar ta ba. Ana samar da shi don zama wani waje na tafiyar da ayyuka kala-kala da kuma amfani da ita a matsayin hanyar samar da kudin shiga ga jaha ko kasa bakidaya. 

Mafi akasarin mutanenmu suna kallon Masana’antar Fim a matsayin wani dandali da za a rika shirya tabargaza da ta’asa da rashin da’a. Sannan duba da ganin yadda sana’ar fim ba ta samu kujerar zama ba a cikin al’ummarmu, wannan ya sa aka gaza samar da wadanda za su bayar da fadakarwa a kan tsarin da kuma yadda za a tafi da shi. Tabbas Masana’antar Fim ci gaba ne ga garin Kano da kuma kasar Hausa. Wannan shi ne hangen da ya sa Malam Ibrahim Khalil yake goyan bayan kawo wannan masana’anta a garin Kano.

Abu na biyu da nake so mu fahimta a kan harkar fim shi ne: Tabbas fim ya yi kaurin suna a kasar Hausa, duba da yadda tarbiyya ta yi karanci a cikin tsarin sa da kuma masu aiwatar da shi. To amma abinda muka manta shi ne, shekarun baya, fina-finai irin su Turmin Danya, Duniya Makaranta, Dan Magori suna daga cikin ayyukan adabi da muke kallo kuma muke amfani da su wajen ilmantarwa da kuma nishadantarwa.

A da abaya, wadannan jarumai su ne a matsayin madubin al’umma wajen samar da tarbiyya da kuma wa’azantarwa. Sai dai kuma cikin rashin sa’a, sai ‘yan zamani suka shigo lamarin suka vata shi. Wannan ya sa aka daina kallon shirin fim din Hausa da kima. 

Yanzu haka muna cikin wani kadami da ko kana so ko baka so, sai an yi shirin fim. Domin kuwa ya zama wani abu na zamani. fim ya zama wata hanya ta ilmantarwa da wayar da kai. Duk da lalacewar masana’antar, har wa yau, akwai fina-finai masu koyar da tarbiyya da wa’azantarwa. Yanzu haka, sana’ar fim ta kai yadda ‘ya’yanmu da ‘yanuwan mu ne suke tururuwa wajen shigar ta.

Kuma wasunsu, suna da kyakkyawan nufi a kan wannan sana’ar. Saboda sun gane cewa yanzu duniya ta canja, idan kana fadakarwa ne ta hanyar rubutu, yawan masu karatu ya ragu. Idan kuma ta hanyar makaranta ne, yara sun daina mayar da hankali kan karatu. Don haka hanya mafi sauki da za ka isar da sako a yau ita ce ta hanyar wasannin kwaikwayo. Wannan ya sa dole ko muna so, ko ba ma so, wasan kwaikwaiyo ya zo kuma dole mu tafi tare da shi a kasar Hausa.

A kokari da hukumomi suke wajen ganin an tsaftace wannan sana’a, shi ne da fari, sai gobnati na janyo mutumin kirki, mutum mai tarbiyya wato Abba El-Mustapha ta ba shi ragamar kawo gyara a cikin wannan masa’anta. Kuma daga farawar sa zuwa yanzu mun ga ci gaba sosai. Sannan yanzu haka, gobnati a tsaye take wajen samar da hanyoyi sabbi da za a tace duk wasu vata-gari daga cikin harkar.

Sannan ana ta kokari wajen samar da shirin fina-finai wanda suke koyar da addinin musulunci da kuma tarbiyya irin wadda ta yi dai-dai da musulunci. Kamar misalin shirin fim din Izzar So  wanda ya qunshi mutane masu ilimin addini wanda kuma suke kawo ayoyin Kurani da Hadithi.

Kirana gare mu shi ne: Ko dai mu hadu a gyara shirin fina-finai a kasar hausa don su zama sun yi dai-dai da al’adunmu da addininmu, ko kuma mu yi shiru mu zuba ido, mu yaqe su, a karshe za a ci gaba da shirya fina-finan, kuma za a ci gaba da amfani da su wajen lalata tarbiyya.

Kuma a karshe matanmu ne da ‘ya’yanmu suke kallo ko mun sani ko ba mu sani ba. Sannan lokaci ya yi da za mu daina nuna fuska biyu: Wato da daddare ka kulle kan ka a daki ka kalli Bollywood, Hollywood, har ma da Nollywood wanda sun fi Kannywood nuni da tsiraici da badala, amma da rana ka fito kana tsinewa ‘yan fim din Hausa. Kai wani hanzari ba gudu ba, kaso 75% na al’ummar kasar hausa suna sanya Satalayi Dish a gidajensu don kallon shirye-shirye na kasashen ketare wanda suke nuna badala wadda tafi ta fina-finan Hausa. Don Allah, akwai abinda ya fi wannan munafurci? 

Ka yarda a gidanka a kalli kasashen ketare amma ba ka yarda a kalli fim ɗin Hausa  ba. Maganar Gaskiya ita ce: Hannunka ba ya ruvewa ka yanke ka yar, dauka kake ka gyara shi. ‘Yan fim din Hausa  ‘ya’yanmu ne, da kannenmu, da iyayenmu, da ‘yanuwanmu. Sannan harshen da ake amfani da shi wajen fim harshenmu ne na Hausa. Don haka mu daina la’antar su, mu daina aibanta su, mu daina allawadai da sana’ar bakidayan ta.

Mu shiga sahun jerin gwanon wanda za su gyara ta don ganin ta samu tsafta. Idan ba ka zo an gyara ta tare da kai ba, wata rana, duk malantarka, duk zafinka, yaronka ko yarinkarka za su iya tashi su ce su idan ba fim ba, ba za su yi komai ba.

A Wannan lokacin ne za ka tuna cewa an gaya maka hakan zai faru. Amma yanzu idan aka tsaftace ta, aka yi mata tsare-tsare na musamman, aka sanya sabbin ka’idoji, to ina tabbatar muku da cewa, dukkanmu muna alfahari da Kannywood da nasarorin da za su iya cimmawa. 

A karshe, ina goyan bayan Malam Ibrahim Khalil a kan ci gaba da neman kafa Masana’antar Fim, da kuma kokarin sa na ganin an tsaftace sana’ar. Sannan ina goyan bayan Shugaban Hukumar Tace Fina-finai, wato Abba El Mustapha a kan kudurinsu na ganin an samar da tsaftatacciyar masana’antar fim a Kano da ma Arewa bakidaya. Sannan ina kira ga ‘yan siyasa musamman Hon. Kofa wanda shi ma yana daya daga cikin wadanda suke kokari wajen ganin an samar da wannan masana’anta a Kano, da su ci gaba da neman wannan tsari don samar da ci gaba a sana’ar fina-finan Hausa. 

Idan Kannywood ta gyaru, Arewa ce bakidaya za ta amfana, hakazalika idan ta lalace, Arewa ce bakidaya a ruwa. Allah ya ba mu ikon fahimta. Amin. 

Inda na yi kuskure Allah ya yafe min, inda kuma na yi dai-dai Allah ya karva daga gare ni ya kuma qarfafa min gwuiwa. Amin. 

Kiru, mai sharhi kan lamuran yau da kullum, ya rubuto daga Jihar Birno. #MuhdKiru