Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta yi sabon shugaba

Daga BASHIR ISAH

A ranar Talata aka rantsar da Hon. Oludaisi Elemide a matsayin sabon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ogun inda ya maye gurbin Olakunle Oluomo wanda ska tsige shi a matsayin kakin majalisar makon jiya.

Yayin zaman majalisar karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar, Bolanle Ajayi wanda ya samu halarcin mambobi 22, Hon. Musefiu Lamidi ya karanto rahoton kwamitin da majalisar ta kafa don binke kan zarge-zargen da ake yi wa Oluomo.

Rahoton Kwamitin ya ce rashin da’ar da tsohon Kakakin ya nuna wa Kwamitin a lokacin gudanar da bincikensa rashin martabaws ne ga Kwamitin da ma Majalisar baki daya.

“Hakan tabbatar da zargin da ake yi masa kamar yadda yake kunshe a cikin sanarwar tsigewar wandabya hada da karkatar da kudade da sauransu,” in ji kwamitin.

Hon Lamidi ya kara da cewa, Kwamitin ya kama tsigaggen kakakin Majalisar da aikata duka laifunka da ake zarginsa, don haka ya bada shawarar a tsige shi.

Bayan kammala sauraron rahoton Kwamitin, daga bisani, an zabi Hon Elemide kan ya zama sabon Kakakin Majalisar inda aka rantsar da shi domin ya ci gaba da jan ragamar Majalisar.

Sabon Kakakin ya yi alkawarin zai yi aiki da gaskiya, kana ya yi kira ga takwarorinsa da su dauki kansu duk daya suke don yi aiki tare wajen ciyar da jiharsu gaba.