Ukraine na zargin wasu jami’anta da wawushe mata kuɗin makamai

Daga BASHIR ISAH

Binciken gwamnatin Ukraine ya bankado cewar wasu jami’an hukumar kula da makaman kasar sun hada baki da takwarorinsu na ma’aikatar tsaro, wajen karkatar da kusan Dala miliyan 40, da aka ware domin sayen makamai.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke tsaka da fafata yaki tsakaninta da Rasha.

Ya zuwa yanzu an gurfanar da mutum biyar a kotu kan zargin yin rub-da-ciki a kan kudin maka kamar yadda masu gabatar da kara suka bayyana.

Kazalika, bayanan gwamnatin Ukraine sun ce ana tsare da wani guda da aka cafke shi a lokacin da yake kokarin tsallaka iyaka don ficewa daga kasar ta Ukraine.

Rahotanni sun ce muddin zargin da ake yi wa jami’an ya tabbata, akwai yiwuwar su fuskanci daurin akalla shekara akalla 12 a kurku.