Majalisar Dattawa ta buƙaci zama da shugabannin tsaro kan tabarɓarewar tsaron ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dattawa ta gayyaci shugabannin tsaro domin su zo a zauna don tattauna matsalar tsaron da ke kara kamari a kasa.

Sai dai, Majlisar ba ta ayyana takamammiyar ranar da jami’an za su bayyana a gabanta ba.

Majalisar ta gayyaci shugabannin tsaron ne bayan tattaunawar sirrin da mambobinta suka yi na sama da sa’o’i uku a ranar Talata, inda suka nuna damuwarsu kan yadda ake samun karuwar sace-sacen mutane da kisa da sauran manyan laifuka.

Jagogaran Majlisar, Michael Bamidele Opeyemi, ya bayyana cewa baki daya sanatocin su 109 kowannensu ya gabatar da kudurin doka kan matsalar tsaro saboda muhimmancinsa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi korafi kan yadda ake samun aukuwar hare-haren ta’addanci da kuma garkuwa da mutane a sassan kasa.

Ya ce, matsalar ta kai yanayin da akan samu mutanen da ke shiga tsakani suna karbar kudaden fansa a madadin barayin mutane.

Daga nan, Akpabio ya yi tir da hare-haren baya-bayan da ‘yan bindiga suka kai Filato da kuma fashewar gas da ta auku a Ibadan, babban birnin jihar Oyo

Ya kara da cewa, Majlisar za ta duba ta tsayar da ranar da shugabannin tsaron za su bayyana a gabanta.