Nijeriya ta nuna rashin jin daɗinta kan ficewar wasu takwarorinta daga ECOWAS

Daga BASHIR ISAH

Nijeriya ta ce ko kadan ba ta ji dadin ficewar da wasu takwarorinta suka ce sun yi ba daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS.

Nijeriya ta bayyana rashin jin dadin nata ne a sanarwar da ta fitar a ranar Litinin ta hannun Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar wanda aka wallafa a shafin X na ma’aikatar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Ambasada Francisca Omayuli ta ce: “Kusan shekara 50 ke nan ECOWAS take aiki don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dimokuradiyya a yankin.

“Nijeriya tana tare da ECOWAS don jaddada tsarin da ya dace da kuma kudurinmu na karewa da karfafa hakki da jin dadin dukkan ‘yan kasashe mambobin kungiyar.”

Kasashen da lamarin ya shafa, Burkina Faso da Mali da kuma Nijar sun ce sun dauki matakin ficewa daga ECOWAS ne saboda ta gaza taimaka musu wurin shawo kan rashin tsaron da ke addabar su da ma sauran kalubalen da suke fama da su.

Sai dai ECOWAS ta ce har yanzu kasashen ba su sanar da ita matakinsu na fita daga cikinta ba a hukumance.