AFCON 2023: CAF za ta yi wa Osimhen gwajin ƙwayar ƙara kuzari

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika (CAF) ta zabi dan Nijeriya Victor Osimhen domin yin gwajin kwaya.

Victor Osimhen ya taka rawar gani wa Super Eagles ta Nijeriya a Gasar Cin Kofin Afirka  da ke gudana wanda ya kai Nijeriya ga saun nasarar yin waje da kasar Kamaru.

MANHAJA ta kalato cewa, CAF ta sanya wa dan wasan ido ne tun baya wasan da suka buga da Guinea-Bissau.

Kazalika, dan wasan FC Nantes, Simon Moses da William Troost-Ekong na daga jerin ‘yan wasan da za su fuskanci gwajin kwayoyin kara kuzari.

Ana gudanar da irin wannan gwajin ne a kan duk wani dan wasan da ake zargin kuzarinsa a fagen wasa ya wuce kima.