Basaja a zaman aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI

Sannunku da jimirin karatun shafin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja! A wannan mako mun kawo muku yadda wasu ma’aurata suke yin basaja a zaman aure. Wanda abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen kawo rikici a gidajen aure har ma idan abu ya yi qamari ya kai ga rusa auren gabadaya.

A makon da ya gabata mun fara kwararo muku bayani ya zu kuma za mu dora a kashi na biyu na wannan maudu’in. A sha karatu lafiya.

Haka su ma mata akwai kawaye da za su dinga cika muku baki mijinta ya yi mata kaza da kaza. Ya kashe mata kudade kaza-kaza. Ko kuma ta dinga nuna irin yadda ta mallake shi yake mata biyayya da sauransu. Ko yadda take dila kishiya ko ‘ya’yan miji ke kuma ki yi sha’awa ki gwada a naki gidan kwabarki ta yi ruwa. Ki rusa aurenki idan ba ki yi sa’a ba.

Ko kuma ki hango ko ki ji labarin wata a wani tamfatsetsen gida ga motoci, ga daula. Ki dinga hangen ke ba ki yi sa’a ba, ki fitini kanki a banza. Wata ma sai ta kashe aurenta saboda wancan hange da take yi ya sa har ta dinga raina mijinta da dukkan samunsa da abubuwan da yake yi mata na kyautatawa.

Amma abinda muka kasa ganewa shi ne, shi fa rogo, rogo ne. Kitse ma, kitse ne. Duk yadda ya yi maka kyau daga nesa, sai ya ba da kai idan ka matso kusa. Don haka mu daina yaudaruwa da kallon kitse a matsayin rogo.

Sannann mun kasa gane cewa shi kowanne miji ko mata da irinsa. Kowanne mutum bai cika goma ba. Duk yadda abokin rayuwarku yake dan Adam ne. Dole akwai inda ya gaza komai kokarinsa. Ku daina hangen rayuwar wasu. Su ma yadda kuke sha’awarsu haka watakila suke ganin kamar ku ma ba ku da matsala.

Kuma kowanne dan Adam da tasa jarrabawar. Misali kamar matar nan da kuka gani tana fantamawa a cikin daular makeken gidan nan. Allah ne kadai ya san wacce jarrabawa Allah ya dora mata. Watakila akwai matsalar dangi ko na uwar miji da ba sa kaunarta, ko kangararren da, ko rashin adalcin miji da sauransu. Amma ke ba ki yi tunanin komai ba sai daular da take ciki. To ki bude idanunki ki gane, wancan kitsen da kike hangowa mai yiwuwa rogo ne. Rogon ma busasshe mai faci.

Haka wasu ma za su iya yi muku karya su nuna muku sam ba su da matsala. Kamar wancan mijin da na kawo misalinsa a sama wanda yake cika baki a kan yadda yake dila iyalansa. Watakila ma fa duk bula ce. Watakila a gidan ma ba shi da katabus. Amma ya cika muku baki ya dora ku a keken bera kuna neman rusa aurenku.

Haka ma mata, musamman masu sayar da kayan mata kan kuranta cewa, mazansu a tafin hannunsu suke. Ke kuma ki je ki yi ta wahalar da kanki sai mijinki ya zama haka. Daga karshe ki tuge igiyar auren naki gabadaya. Hattara da kallon kitse a matsayin rogo.

Abu na gaba kuma, a sani kowanne dan adam da irin yadda yake rayuwarsa. Wani ba za ka iya canza shi ya koma yadda kake ko kike so ba. Sai a yi hakuri da shi. Don ba zai rasa wasu abubuwa kuma masu kyau wadanda kai kake so ba daga wajensu.

Sannan kuma ku sani, akwai sirrika birjik a gidajen aure wadanda ma’aurata ko danginsu da wuya su sani. Amma don ba su fada ba, ba ya nufin babu matsaloli. Kawai su sun fi ku godiyar Allah ne shi ya sa ba sa korafin. Sun rufa wa kansu asiri sun zauna lafiya.

Misali ki ga wata mace mijinta yana ta lallava ta ina ka sa, ina ka ajiye. Ke kuma ki ji duk Duniya ta yi miki zafi saboda ke naki mijin ba ya yi miki haka. To ki sani, watakila ita wannan matar komai na gidanta ita ta dauki nauyinsa. Mijinta ba ya kashe mata ko sisi daga kudinsa. Misali ne kawai na bayar. Ban ce ko’ina haka ne ba.

Amma kin ga idan ba ta fada miki ba, ai ba za ki sani ba ko? Ke kuma daga ganin wannan sai ki je ki daga wa mijinki hankali saboda ba ya miki haka. Haba ‘yaruwa! Shi fa rogon nan matukar yana nesa ba ki zo kusa kin kashe kwarkwatar idanunki ba za ki yi ta ganinsa a kitse. Kuma za ki yi ta yaudaruwa da wahaluwa a rashin binciken hakikanin lamarin.

Haka maza masu kushe matan Hausawa su dinga yi wa matan kanuri ko wasu kabilun kallon kitsen rogo su ma su yi hattara don watakila kallon kitsen rogo ne. Don haka kowanne bangare mata da maza a dinga gode wa Allah da abokan rayuwa. Bissalam.