An cafke uwa kan jefar da jaririyarta cikin rafi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ‘Yan Sanda ta damke wata mata da ta jefa jaririyarta mai watanni biyar a duniya a cikin kogi da nufin kashe ta.

Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta cafke matar mai shekaru 30 a duniya ne kan zargin yunkurin halaka jaririyar a kogin RSS da ke Sagamu.

A yammacin ranar Litinin ne ta jefar da jaririyar a ruwa domin ta nutse, amma wani wanda da ya ga abin da ta yi da ke kusa da wurin ya taimaka wajen ceto ta.

Sanarwa da kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, ya aikewa manema labarai a ranar Litinin ta ce an kai jaririyar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo da ke Sagamu domin ba da kulawa.

Sanarwar ta kara da cewa, “jaririyar mai watanni biyar, yanzu haka na cikin kwanciyar hankali bayan wani mai suna Olusola Sonaya da ke yankin RSS River a Sagamu, ya ceto ta daga nutsewar bayan jefa ta da mahaifiyarsa ta yi da gangan a cikin rafi.

“An kama mahaifiyar kuma a halin yanzu ana kan sa ido don tabbatar da lafiyar kwakwalwarta.

“Ana kuma kokarin gano ’yan uwa ko mijin don mika musu jaririyar saboda su ba ta kulawar samun jin dadin da ta dace.”