19
Feb
Daga AISHA ASAS Malam Sagir Baban Khausar shahararren mawaƙin Hausa wanda waƙoƙinsa suka fi mayar da hankali fannin ilimantarwa, faɗakarwa da nuni cikin nishaɗi. A wannan makon jaridar Manhaja ta samu damar tattaunawa da shi don kawo wa masu karatu wani abu da ba su sani ba game da shi. Ga dai yadda wakiliyar ta tattauna da shi: Mu fara da jin tarihin ka.Assalamu alaikum. Da farko dai suna na Sagir Mustapha Ɗanyaro, jama’a sun fi sani na da Sagir Baban Kausar. Ni haifaffen Lungun Liman ne da ke gidan Liman a Kabala Coastain da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta…