Al’jabi: Damisar da ta kamu da Annobar Korona

Daga UMAR M. GOMBE

An samu wata Damisar yankin qanqara mai kimanin shekara biyar da haihuwa mai suna NeeCee da cutar Korona Baros, bayan da aka yi ma ta gwajin qwayar cutar a farkon wannan makon.

Gwajin wadda a matakin farko ya nuna cewa ta na dauke da qwayar SARS-CoV-2, wadda ke rikidewa zuwa COVID-19 ga bil’adama. Mujallar Courier-Journal ce ta ruwaito wannan abin al’ajabi da ya faru a wani gidan Zoo dake garin Louisville a Jihar Kentucky ta Qasar Amurka.

A ranar Juma’ar nan ne hukumar gidan Zoo din ta sanar da hakan, ta na mai cewa an yi wa  damisar tare da wasu biyu gwajin qwayar cutar, bayan da aka ga waxansu alamu na annobar Korona tattare da su, amma sakamakon NeeCee din ne ya fito a yanzu.

A halin yanzu dai ana ci gaba da jiran sakamakon gwajin da aka yi wa ragowar damisoshin guda biyu wadanda dukkan su maza ne, na cikin dusar qanqara kamar yadda mujallar ta Courier-Journal ta ruwaito.

“Dukkan damisoshin ba ma su yawan laulayi ba ne, su na da cikakken lafiya sannan su na cin abinci yadda ya kamata kuma akan lokaci. Don haka lamarin ya zama abin mamaki qwarai, kasancewar kuma akwai dokokin da aka sanya wa dukkan ma’aikatan gidan Zoo din. Kuma ana bin matakan da suka hada da gwajin zafin jiki da sanya safar hannu da dukkan matakan kariya daga annobar Korona kafin yin mu’amala da dabbobin namu bakidaya,” inji wani masanin harkokin dabbobi na gidan zoo din mai suna Zoli Gyimesi.

Gyimesi ya qara da cewa, “baya ga xaukar waxancan matakan domin baiwa dabbobin kariya, akwai tambayoyin da ma’aikatan kan amsa a kullum kafin a amince ma su shiga bakin aiki”

“Mu na ci gaba xaukan dukkan matakan kariya da suka kamata, wajen baiwa baqin dake zaiyarar wannan gidan zoo da kuma dabbobin mu bakixaya,” a cewar Shugaban Zoo xin, Mista John Walczak.

Kodayake tun da farko Hukumar Gidan Zoo xin ta bayyana cewa babu wata fargabar da ake da ita na cewa dabbobin dake xauke da qwayar cuta za su iya raba ta ga ‘yan Adam, sai dai su ka ce akwai yiwuwar a qara xaukar wasu matakan da samar da cikakken kariya ga kowa.

Tuni dai aka fitar da damisoshin su uku daga sashen yawon buxe ido na gidan zoo xin aka killace su, har zuwa lokacin da sakamakon ragowar zai iso, da kuma sa ran cewa NeeCee ta samu lafiya daga cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *