‘A Tribe Called Judah’: Fim ɗin Nollywood da ya yi fito-na-fito da Hollywood (2) 

Daga AISHA ASAS

Fim din na Turanci da za mu iya fassara ci da ‘Wata Al’umma da ake kira Judah’, labari ne da ya shafi rayuwar wata mata da mahaifinta ya kore ta sakamakon ta yi cikin shege, duk da cewa a al’adar Bayare bai zama illa yin ciki kafin aure ba, asalima wasun su da yawa sun fi goyon bayan yin cikin kafin auren don tabbatar da za a iya samun haihuwa a auren, sai dai yayin da tsautsayi ya gitta, mace ta hadu da mayaudari ya mata ciki ya ki auren ta, ko wata matsala tasamu da auren ya ki yiwa to fa abin zai tsaya kan matar ne, wato ta yi cikin shege.

Ita ma wannan matar mai suna Judayah wadda shahararriyar jaruma kuma mai shirya fim Funke Akindele wadda aka fi sani da Jinnefa ta hau wannan rol din, sanadiyyar wannan cikin shege ya sa ta zama korarriya a wurin mahaifinta, tare kuma da yafe ta. Wanda hakan ya sa ta gina wa kanta rayuwa wani wurin daban da rayuwa ta kaita ga samun ‘ya’ya biyar, amma kowanne daga cikinsu ubansa daban.

Hallayar ‘ya’yan ta bambanta, domin akwai barawo, dan daba, sagartace, sai kuma yayensu da daya ke aikin gadi, yayin da daya ke aiki a kamfanin siyar da kayan daki. Sai dai halin rashin lafiya da mahaifiyar tasu ke ciki ne ya sanya su karkata ga halin daya daga cikinsu, wato barawon don nema wa mahaifiyar tasu kudin da za a yi mata dashen koda.

Matsaloli suka gudana wanda daga karshen fim din dai suka samun nasarar guduwa ta jirgirin ruwa bayan da wanda suka kwashe wa kudin na neman su, su kuma sun rasa babban yayan nasu ta sanadiyyar wannan fashin.

Labarin fim din ba shi ne ya fi daukar hankali ba kamar yadda jaruman suka numa kwarewa, na farko kenan, wanda hakan zai iya tabbatar wa mai kallo sun samu horo irin wanda ake bukata.

Sai abu na biyu, wanda zan iya cewa a bangarena zan iya yin jinjina ga fim din, kuma zan iya amincewa idan aka ce shi ne kashin bayan nasarar fim din, wato yadda aka cire tsoro, aka baza kudade don yin aikin fim din yadda ya dace, tare kuma da amfani da cigaban zaman. 

Zan bada misali da bindigar da aka yi amfani da su, sun yi kama da na gasken sabanin wadanda muke gani a finafinai da ko yaro qarami zai iya gane ba na gaske ba ne, sakamakon kamar da suka yi da irin wadanda yake amfani da su na wasa.

Haka ma idan aka koma bangaren sutura, nan ma zan iya cewa an kwatanta adalci a fim din. Sai kuma babba daga ciki wanda ya fi komai jan hankali shi ne, editin din fim din, wanda zan iya cewa, tabbas idan har zan fadi fim kwaya daya da ya yi kamanceceniya da na masu jan kunne to wannan ne.

Mai karatu zai iya daukar misalin yadda suke harba bindiga, da yadda aka samo fitar jini daga jikin wanda aka harba, tabbas zai iya amincewa da an samu canji a finafinan mu. 

Abu na karshe da ya zama babban abin dubawa ga masu shirya finafinai shi ne, salon yadda ta bazama tallata fim din tare da fitowa da hanyoyin da za ta kwadaita wa mutane fim din tun kan ya fito, wanda tabbas zan iya cewa iya wannan kawai ya kawo wani kaso mai nauyi a nasarar da ta samu, wanda a cikin makonni uku kacal ya kafa wannan tarihi.

Wadda ta shirya fim din jaruma ce a masana’antar finafinai ta Kudu, a bangaren Turanci da kuma Yarbanci, kuma darakta kuma furodusa, Funke Akindele.

Wannan ba karamin cigaba ba ne ba a iya ita kanta ba ko masana’antar finafinai ba, har ma ga kasa bakidaya, wannan ya sa Shugaban Kasa Bola Tinubu ya jinjinawa jarumar kuma darakta da ta fi kowane daraktan fim samun kudi a harkar fim, ya kuma yaba mata kan namijin kokarin da ta yi a fim din na ‘A Tribe Called Judah’ sannan ya bayyana jin dadin sa na kai harkar fim inda bai taba kaiwa ba.