Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (4)

Daga AISHA ASAS

A ci gaba da bayyani kan yadda za a iya ba wa fata kulawa a lokacin sanyi, a yau darasin namu zai tabo bangaren gashi. Sai dai kafin nan zan so mu yi waiwaye don tunatar da mai karatu abinda darasin namu ya kunsa a baya.

Mun soma da bayanin yadda fata ke shiga mawuyacin hali a lokutan sanyi, wanda muka ce da taimakon sanin yadda ake iya kula da ita, za a samu sauqi daga irin lalacewar da ta ke yi a lokacin sanyi.

Sannan mun kawo hanyoyin da za a iya kula da fatar daga ababen ci da na amfani, kafin mu dira kan kafa wadda ita ma na daya daga cikin wuraren da ke jigata a lokacin sanyi. Wanda a nan ne muka dasa aya a satin da ya gabata.

Gashi: babu wani lokaci da gashi ya fi bukatar kulawa kamar lokacin sanyi, domin a lokacin ne ya fi yawan karyewa da kuma saurin bushewa. Duk da cewa ababen da muke ci ne ababe mafi rinjaye da suke tasiri a gyaruwa da kuma lalacewar gashin kanmu, wannan na daga dalilan da ya sa ingantacen abinci da kayan itace ke layin farko na bayani ga wadda ta ce tana son gashinta ya gyaru. Sai dai yanayi ma na taka tasa rawar a lokuta da dama, don haka yake da matukar muhimmanci a yi amfani da wadannan matakai a lokacin sanyi don ba wa gashi agaji;

Shan ruwa: kadan daga cikinmu ne kawai suka san yawan shan ruwa a lokacin sanyi na rage yawan karyewar gashi.

Turara gashi: abinda bature ke kira da ‘steaming’, wanda ake amfani da na’uwa mai sakin zafi ana turare gashin, kuma abu ne mai sauqin kudi ko a wurin jingar yin sa a wuraren gyaran kai. Matuka yana taimakon gashi a irin wannan lokaci na sanyi.

Yawan shafa mai: Kasancewar lokacin sanyi na saurin busar da jiki, gashi na bukatar mai mai matski da zai sa ya zama a jike a kodayaushe, don gujewa abinda zai iya sa ya dinga zuba.

Rufe kai: yawan saka dankwali ko hula na da matuqar muhimmanci ga wanda yake son ba wa gashinsa kariya daga sanyi. Wannan zai taimaka wurin hana shi kara bushewa, tare da hana kwayoyin cuta da ka iya illa da iskan hunturu zai kwaso ya kai ga gashin.

Yin kitso: ba abu mai kyau ba ne za ma da kai babu kitso a lokacin sanyi, domin iska ya fi samun shiga sosai idan kan yana a tsefe. Sannan za a fi yawan taje shi Idan babu kitso, don haka yawan zubar sa zai fi na idan an kitse shi.