Dandalin shawara: Mijina ba ya iya gamsar da ni kuma na rasa ta yadda zan sanar da shi

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Malama barka da rana. An wuni lafiya. Ya iyali. Allah shi taimaka maki, amin. Ni dai tambaya ta dai ina neman yadda zan sanar da mijina ba ya wadatar da ni a shimfida. Wato shi dai mutumin kirki ne sosai, yana iya kar kokari ga iyalinshi, tun ma ba akan abinci ba daidai gwargwado muna ci mu koshi. Yana wasa da dariya da dai sauran abubuwa.

To amma matsalar ba shi da wani karfi. Tun da aka kawo ni gidansa a matsayin budurwa babu jimawa na daina koshi da rayya sunnah da muke yi, da farko na dauka haka ne ga kowacce mace, sai daga baya dai na fahimci nawa mijin ne haka.

Yanzu haka har mun haihu daya, sai dai duk marmari da nake yi da dare da na tuna yadda yake sai na ji ba dadi a raina, saboda yadda ki ka san an lasa wa mai jin yunwa miya a baki, haka nake ji lokacin da ya gama. Kuma irin kyautatawar da yake min ya sa nake jin nauyin gaya masa.

Ki ba ni shawara yadda zan magance wannan matsala, ko da ta rage sha’awa ce ko ma daidaita da shi. Na gode. (Rubutun wannan sakon ya zo a cakude, da kyar na iya gane wasu daga ciki. Da fatan na fitar da abinda mai tambayar ke bukata).

AMSA:

Idan har mun samu tambayar daidai, abu na farko da zan fara da shi ne, ba ki yi laifi ba don kin bukaci fiye da abinda mijinki ke ba ki, kamar yadda masana ilimin jima’i suka ce, sha’awa ta kasu har kashi uku, kuma haka mutane suka kasu uku a bangaren sha’awa.

Don haka abu ne na halitta ba wai kai ke sa wa kanka ba. Yakan yiwu taki karfin sha’awar ce ta rinjaye ta mijinki, kuma yakan iya yiwa raunin nasa na da alaka da rashin lafiya ko rashin kula da kai a matsayinsa na namiji. Sai dai ba za ki iya gane wa ba har sai kin yi magana da mijin naki.

Ki sani, aure fa ana yin sa ne domin kame kai da kuma rufe ido daga kallon haram. Shi ya sa addini ya ba wa miji damar zuwa ga matarsa a duk lokacin da ya so, idan ka cire lokacin da ta ke jinin al’ada. Sannan ya ba wa mata damar tambayar mazajensu hakkinsu a duk lokacin da suka bukaci hakan, sannan ya gargadi maza kan tauye wa matansu hakkin nasu, sai bisa ga babban dalili.

Ma’ana dai aure wuri ne na kawar da sha’awa wadda za ta hane ki da zina. Idan kuwa ba kya samun yadda ki ke so, kinga akwai yiwar shedan ya fara yi maki rada a kunne. Wanda hakan ne ake gudu.

Rashin sanar da mijin naki ba ta inda zai amfane ki, domin yakan yiwu matsala ce qarama da za ku iya kawar da ita, misali, takan iya yiwa karfinsa ya fi hakan, amma kila yana da basiri ko makamantan curutan da ke raunana namiji, albarkacin kin yi gum da bakinki ba zai taba gane hakan ba, a tunanin sa yadda ya gamsu kema haka ki ka gamsu. Kinga kuwa ba zancen ya nemi magani, ko ‘yan dabarun karawa namiji kuzari.

Kamar yadda ki ka ce, kyautatawar da yake yi maki ne ke sa ki ganin kamar cin fuska ne sanar da shi hakan, sai dai akwai ‘yan dabaru da mata ke bi wurin sanar da irin wannan matsala ga mazajensu, ma’ana cikin kauli mai taushi da kuma dabara. Wanda idan zai fahimci maganar za ta zama kamar tsananin soyayyar da ki ke masa ne ta janyo hakan ba wai kina nuna gazawarsa ba.

Ta sanar da shi ne za ki iya gane matsalar, domin matukar kin aza shi yadda ya dace, kaso mai yawa na maza wawaye ne akan matansu ko matan da suke mu’amala da su, zai yi matukar kokari wurin ganin ya samar da hanyar da zai cika maki muradin ki, wanda ta hakan za ki iya gane matsalar inda ta dosa, domin idan har ya kasa samun mafita ta dindindin to kenan akwai matsala, don haka a nan zan iya cewa a nan ne za ki yi tunanin da zai iya fitar da ke.

Idan har za ki iya hakuri da shi a hakan ba tare da kin cutatar da kanki da zai sa ki fara kallon zina a matsayin mafita ba, wannan tsakanin ki da Allah. Idan kuwa kin ji ba za ki iya rike kanki ba, addini ya ba ki damar neman rabuwa don ki auri daidai ke. Amma hakan zai zo ne bayan tabbatar da qarfin sha’awarki ta zarta ta mijinki. Babu kunya a abinda Allah Ya halasta. Lallai Allah ba Ya kunya kan gaskiya.

Zance na karshe, ina so in tunatar da ke kan sha’anin rayuwa. Bakidaya rayuwa jarrabawa ce, bai zai yiwu ta kowanne bangare na rayuwar Musulmi ta zama yadda yake so ba, dole a jarrabta shi a wasu bangarorin. A tawa fahimta Allah Ya ba ki miji nagari, sai dai ya rage ki ta bangaren kwanciyar aure, don haka yadda za ki yi da wannan jarrabawa tana hannunki. Sai dai zan kara fada, kafin ki yi hakuri sai kin tabbatar kina iya kame kanki, domin zama kuma ki fada zina shi ma faduwa jarrabawa ne. Allah ne mafi sani.