Matsalar tsaro: Majalisar Dattawa za ta sammaci Ministan Abuja

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dattawa ta ce ta kimtsa domin gayyato Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya zo ya yi bayani game da tabarbarewar tsaro a Birnin Tarayya.

Sanata mai wakiltar Birnin Tarayya a Majalisar, Ireti Kingibe ce ta bayyana haka yayin wata tattaunawa da tashar Channels TV ta yi da ita a ranar Lahadi.

Ta ce idan majalisar ta dawo bakin aiki, za a gayyato Wike a matsayinsa na Ministan Abuja don ya zo ya yi bayanin matakan da yake dauka domin dakile matsalar taro a birnin na tarayya.

A cewar Sanatar, “Ina da yakinin za a gayyace shi. Amma amsawa ko kin amsar gayyatar wani abu ne daban. Sai dai a matsayinsa na babban shugaban tsaro na FCT, dole ya zamana yana da tsari.

“Wajibi ne ya yi mana bayani mu ‘yan kwamiti, musamman ni, tsare-tsaren da ya shirya amfani da su don kare rayukan al’umar yankin Abuja.

“Dole ne a samu tsare-tsare a tsakaninsa da Kwamishinan ‘Yansada da shugaban DSS” don dakile matsalar tsaro a Abuja, in ji Sanata Iteti.

A baya-bayan nan, rahotanni daga yankin Abuja sun ce ana fama da matsalar tsaro, musamman garkuwa da mutane a birnin na tarayya.